Kano: Daina Amfani da Soshiyal Midiya da Wasu Sharuɗa da Kotu Ta Kafawa Murja Kunya

Kano: Daina Amfani da Soshiyal Midiya da Wasu Sharuɗa da Kotu Ta Kafawa Murja Kunya

  • Babbar kotu a jihar Kano, ta ba fitacciyar ƴar TikTok, Murja Kunya, umarnin daina amfani da soshiyal midiya
  • Wannan umarnin ya biyo bayan bukatar beli da ƴar TikTok din ta gabatar gaban kotun, wanda Mai shari'a Nasiru Saminu ya amince
  • Sai dai Saminu ya gargadi Murja Kunya cewa ƴan sanda za su sake cafke ta idan har ta karya wannan sharaɗi da kotu ta kafa mata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wata babbar kotun jihar Kano ta haramtawa fitacciyar 'yar TikTok, Murja Kunya, amfani da soshiyal midiya har zuwa lokacin da za a kammala shari'arta.

Kotu ta kafa wa Murja Kunya sharadin amfani da soshiyal midiya
Kano: An ba 'yan sanda damar kama Murja Kunya idan ta yi amfani da soshiyal midiya. Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: Facebook

Kotu ta ba da belin Murja Kunya

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa kotun, karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu a ranar Litinin ta bayar da belin Murja Kunya, a kan kudi N500,000.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta sake daukar mataki kan 'yar TikTok, Murja Kunya, ta fadi dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yar TikTok din dai ta nemi beli ne biyo bayan umarnin da kotun shari’ar Musulunci ta Kano ta bayar na cewa likitan tabin hankali ya duba lafiyarta.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Saminu ya ce sharudan belin sun hada da kawo mutane biyu da za su tsaya mata.

An ba 'yan sanda damar kama Murja

Kuma dole daya daga cikin mutanen ya kasance dan uwanta, yayin da dayan mutumin ya kasance ya mallaki fili a karamar hukumar Kano.

Rahoton jaridar Aminiya ya nuna cewa Alkalin kotun ya hana Murja Kunya amfani da soshiyal midiya har sai an yanke hukunci kan shari'ar.

Alkalin kotun ya ce:

"Duk wani yunkuri na keta dokar da aka kafa mata zai tilastawa kwamishinan 'yan sandan Kano ya kama Murja tare da dawo da ita gaban kotu."

Kara karanta wannan

Kano: Fitacciyar ƴar TikTok, Murja Kunya, ta shigar da sabuwar buƙata a babbar kotun tarayya

Kotu ta nemi yin zama da Hisbah

Alkalin ya kuma ba da umarnin cewa:

“Lauyoyin wadanda ake tuhuma, da Alkalin Alkalan, da wakilai daga hukumar Hisbah, da kwamishinan ‘yan sanda za su hallara gaban kotu.
"A yayin zaman, muna fatan za su gyaran dokar da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi amfani da ita domin ba wannan kotun damar yanke hukunci.”

Don haka kotun ta dage zaman har zuwa ranar 16 ga Mayu, 2024, domin ci gaba da shari’ar.

Zargin kisa: Kotu ta ba da belin Oyebanji

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wata kotun majistare da ke Kwara, ta ba da belin daya daga cikin wadanda ake zargi da kashe Sarkin Kwara, Oba Peter Aremu.

Barista Udeh, lauyan Olowofela Oyebanji, wanda ake zargin, ya sanar da kotun cewa wanda yake karewa na fama da rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel