Majalisar dattawan Najeriya
‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Sanata Dino Melaye ya saki satifiket din tsira daga hannun Tinubu, yayin da yake martani ga halin da ake ciki a kasar.
Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na korar shugaban hukumar kare masu sayen kayayyaki ta tarayya, Babatunde Irukera.
Shugaba Tinubu ya ce Babatunde Irukera ba ya iya aiwatar da aikinsa yadda ya kamata, shi ya sa aka tsige shi daga shugaban hukumar kare masu amfani da kaya ta FCCPC.
Majalisar ta yi mamakin yadda kamfanin karafa na Ajaokuta da NIOMCO ke ci gaba da tabarbarewa duk da zargin biyan $496m ga ‘yan kwangila tsakanin 2008 zuwa yanzu.
A lokacin Muhammadu Buhari, an yi ta buga kudi domin a ba gwamnatin tarayya aro. ‘Yan majalisar dattawa sun nada Sanatoci da za su binciki bashin da Buhari ya karbo.
Sanata mai wakiltar Funtua a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Muntari Ɗandutse, ya ce wasu miyagu sun halaka kaftin da sojoji biyu, ya faɗi mafita.
Majalisar dattijai a ranar Talata, ta tabbatar da nadin shugaba Bola Tinubu na Hafsat Bakare, a matsayin daraktar hukumar kwararru ta kudi ta Najeriya (NFIU).
Maganganun da shugaban majalisar dattawa ya yi a kan gwamnonin jihohi ba gaskiya ba ne. Sanata Godswill Akpabio ya bada hakuri ta bakin mai magana da yawunsa.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya ce albashinsu bai isansu a Najeriya, Ben Kalu bayyana wannan ne a ranar Litinin kamar dai yadda Punch ta fitar da labarin.
Majalisar dattawan Najeriya
Samu kari