Cushe a Kasafin Kudi: Sanata Ya Tabbatar da Karbar Naira Biliyan 1 Na Ayyukan Mazaba

Cushe a Kasafin Kudi: Sanata Ya Tabbatar da Karbar Naira Biliyan 1 Na Ayyukan Mazaba

  • Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa ya bayyana cewa ya karbi Naira biliyan daya domin gudanar da ayyuka a mazabarsa
  • Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Seun Okinbaloye a shirin ‘Mic On Podcast’ a gidan talabijin na Channels
  • Bayanin Nwoko na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-ku-ce kan zargin da Sanata Abdul Ningi ya yi na an yi cushe a kasafin kudin 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Sanata Ned Nwoko, sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, ya bayyana cewa ya karbi Naira biliyan daya daga kasafin da 'yan majalisu ke samu domin gudanar da ayyukan mazaba.

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Nwoko, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Mic On podcast’ wanda dan jarida Seun Okinbaloye na Channels TV ya ke gabatarwa.

Ned Nwoko ya magantu kan zargin cushe a kasafin kudi
Ned Nwoko ya ce tasirinsa ya taimaka masa wajen samun karin kudaden ayyukan mazaba. Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa bayanin sanatan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da bin diddikin yadda ‘yan majalisar tarayya ke ware kudaden ayyukan mazabu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bin diddigin ya samo asali ne bayan zargin da Sanata Jarigbe Jarigbe ya yi na cewa wasu “manyan” sanatoci sun karbi Naira miliyan 500 domin gudanar da ayyuka.

Jarigbe ya magantu ne bayan Sanata Abdul Ningi, wanda a yanzu aka dakatar da shi, ya yi ikirarin cewa an yi cushen sama da naira tiriliyan uku a kasafin 2024.

Kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito, ya ce:

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi ya haifawa majalisar dattawa fushin kungiyoyin Arewa

"Abin da ke faruwa a yanzu shi ne, sanata na amfani da tasirinsa da sanayyar mutane wajen nemo kudin da zai yi wa 'yan mazabarsa aiki.
“Mafi kyawun tsarin da zai kawo karshen wannan rashin daidaiton shine a samar da kudi daya ga kowanne sanata. Misali a ce kowane sanata ya samu naira biliyan daya."

- Sanata Ned Nwoko

"Kudin mazaba ne na karba" – Sanata Nwoko

Da aka tambaye shi ko ya karbi kudi har Naira biliyan daya, Sanatan ya tabbatar da cewa ya karba.

Ya jaddada cewa yana karkatar da kudin ne ga ayyukan ta yadda al’ummar mazabarsa za su amfana tare da danganta tasirinsa a wajen samar da irin wadannan ayyuka.

Sanata Nwoko ya ce:

“Tabbas na karba. Amma wannan karfin tasiri na ya jawo hakan, kuma kudin na mazaba ne ba na amfanin kai na ba."

"Ba daya muke a majalisa ba" - Sanata Ndume

Kara karanta wannan

Gaza: Bam ya kashe ‘yanuwa 36 lokacin shirin sahur a dauki azumin Ramadan

A wani labarin, Ali Ndume, bulaliyar majalisar dattawa, ya bayyana cewa wasu shugabannin majalisar na samun kaso mai yawa na ayyukan mazabu.

Legit Hausa ta ruwaito cewa, Sanata Ndume ya nuna kuskuren kalaman Sanata Abdul Ningi na cewa an yi cushe a kasafin kudin 2024, yana mai ikirarin cewa kowanne sanata ya san matsayinsa a majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel