Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Kwankwaso Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga 'Yan Majalisun Arewa

Zargin Cushe a Kasafin Kudi: Kwankwaso Ya Tura Sako Mai Muhimmanci Ga 'Yan Majalisun Arewa

  • Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi magana kan batun zargin yin cushe a kasafin kuɗin shekarar nan ta 2024
  • Jigon na jam'iyyar APC a jihar Kano, ya buƙaci ƴan majalisun da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya da kada su bari batun ya raba kansu
  • Ya yi kira a gare su da su mayar da hankali wajen ganin sun kawo ci gaba mai amfani ga jama'ar da suke wakilta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jigo a jam’iyyar APC a jihar Kano, Illyasu Musa Kwankwaso, ya buƙaci ƴan majalisun tarayya da suka fito daga yankin Arewa da su haɗa kansu.

Musa Kwankwaso ya nemi ƴan majalisun da kada su bari rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, sakamakon zargin yin cushe a kasafin kuɗin shekarar 2024, cewar rahoton jaridar PM News.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gana da ƴan takara 2 da ƙusoshin APC kan muhimmin batu a Villa, bayanai sun fito

Kwankwaso ya shawarci 'yan majalisun Arewa
Musa Iliyasu Kwankwaso ya nemi 'yan majalisun Arewa su hada kansu Hoto: Musa Sale Danzaria
Asali: Facebook

A maimakon haka, sai ya buƙace su da su ba da lokacinsu da ƙarfinsu kan yadda za su jawo ayyukan ci gaba zuwa mazaɓunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, ranar Lahadi, 17 ga watan Maris, 2024, rahoton jaridar Thewillnews ya tababtar.

Wace shawara Kwankwaso ya ba 'yan majalisu?

A cewarsa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana da niyyar kawo ci gaba mai ma’ana a faɗin jihohin Arewa 19.

Kwankwaos ya buƙaci ƴan majalisun da su nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Tinubu, ta hanyar ƙara nuna himma wajen ci gaban yankin Arewa.

A cewarsa, ƴan majalisar za su iya samar da ci gaba a Arewa ne kawai idan suka guji ƙiyayya a tsakaninsu sannan suka zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Kara karanta wannan

Rayuwa ba tabbas: Direba ya fadi ya rasu yana tsaka da tuka dalibai zuwa makaranta

Ya yi nuni da cewa batun cushe a kasafin kuɗin wanda har yanzu ba a tabbatar da shi ba, bai kamata ya kawo rashin jituwa da rashin haɗin kai a tsakanin ƴan majalisar ba.

Kwankwaso, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya ta hanyar yi mata addu’o'i, inda ya yi fatan cewa wahalar da ake fama da ita a ƙasar nan za ta zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Ningi ya yi murabus daga muƙaminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Abdul Ningi, ya yi murabus daga muƙamin shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa.

Sanatan ya haƙura da shugabancin ƙungiyar ne biyo bayan dakatar da shi da majalisar dattawa ta yi kan zargin yin cushe a kasafin kuɗi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel