Bayan Saukar da Kai da Amsa Gayyatar Majalisa, Wike Ya Fadi Gaskiyar Lamarin Rashin Tsaro

Bayan Saukar da Kai da Amsa Gayyatar Majalisa, Wike Ya Fadi Gaskiyar Lamarin Rashin Tsaro

  • Bayan amsa gayyatar Majalisar Tarayya, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana gaskiyar kan garkuwa da mutane
  • Wike ya ce babu wani yanki ko al’umma a fadin duniya da basu fama da wani nau’i na rashin tsaro da yake addabarsu
  • Ministan ya bayyana haka ne ga ‘yan jaridu jim kadan bayan ganawa da mambobin Majalisar kan matsalar tsaron

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi alkawarin inganta tsaro a birnin bayan amsa gayyatar Majalisa.

Sai dai Nyesom Wike ya ce babu wani yanki a duniya da babu rashin tsaro inda ya ce zai yi wahala a iya dakile matsalar tsaro gaba daya.

Kara karanta wannan

Barazanar kisa: Gwamnan PDP a Arewa ya ba Remi Tinubu hakuri, ya daukar mata alkawari

Wike ya bayyana gaskiyar lamari kan dakile matsalar tsaro a Abuja
Nyesom Wike ya ce zai yi wahala a dakile matsalar tsaro baki daya. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Wike ya fadi gaskiya kan matsalar tsaro

Wike ya ce babu wani yanki ko al’umma da babu wani nau'i na rashin tsaro inda ya ce babban abin yi shi ne rage matsalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da ‘yan jaridu a Abuja jim kadan bayan ganawar sirri da Majalisar Tarayya.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar Tarayya ta gayyaci Wike tare da kwamishinan ‘yan sanda, Bennet Igwe a Abuja.

Wike ya ce ganawar da ta dauki kusan awanni hudu sun tattauna muhimman abubuwa masu amfani yayin ganawar, cewar Daily Trust.

Ya ce da kansu mambobin Majalisar sun amince da cewa tabbas an samu ci gaba wurin inganta tsaro a birnin idan aka kwatanta da kwanakin baya.

Nasarar da aka samu kan tsaro a Abuja

Ya kara da cewa cafke kasurguman ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo ya yi matukar tasiri wurin inganta tsaro a fadin birnin da kewaye, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu da CP sun sa labule da sanatoci a zauren majalisar tarayya, bayanai sun fito

“Mafi yawan garkuwa da mutane da ke faruwa shirya shi ake yi da mutane wanda suke yin wata yarjejeniya kafin garkuwar.”
“Misali ka na da direba ko mai aiki a gida, da su ake hada baki domin yin garkuwa da kai, menene ya kamata mu yi? Abin yi shi ne tabbatar da an ceto wanda aka sace”

- Nyesom Wike

An cafke kasurgumin dan bindiga

A baya, mun ruwaito maku cewa rundunar ‘yan sanda a birnin Abuja ta cafke wani kasurgumin dan bindiga.

Rundunar ta yi nasarar cafke shi ne bayan samun bayanan sirri da kuma saka makudan kudade ga wanda ya yi sanadin kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel