Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Ta Yi Martani Kan Harin, Ta Fadi Matakin Dauka

Kisan Sojoji 16: Majalisar Dattawa Ta Yi Martani Kan Harin, Ta Fadi Matakin Dauka

  • Majalisar dattawa ta nuna fushinta kan kisan gillar da aka yi wa jami'an sojoji 16 a wani ƙauyen jihar Delta
  • A cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ta yi Allah wadai da salwantar da rayukan sojojin da aka yi
  • Majalisar ta buƙaci a tabbatat da cewa miyagun da suka aikata wannan ɗanyen aikin sun fuskanci hutuncin da ya dace da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa jami’an soji 16 na ‘Operation Delta Safe’ a ƙauyen Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.

An halaka sojojin ne yayin da suke aikin kwantar da tarzoma a tsakanin wasu ƙauyuka guda biyu na ƙaramar hukumar da ke rikici da juna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rage mugun iri bayan sun ragargaji 'yan ta'adda

Majalisa ta yi martani kan kisan sojoji 16
Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan sojoji 16 a Delta Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

A yayin farmakin dai an halaka kwamandan rundunar, wasu manyan jami'ai guda uku da sojoji 12.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Dattawa a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ta ce tilas ne a hukunta waɗanda suka aikata wannan mummunan laifin, cewar rahoton jaridar Leadership.

Me majalisa ta ce kan kisan sojojin?

A cikin sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojojin Najeriya, Sanata Abdulaziz Yar’adua, majalisar ta yi nuni da cewa ba za a manta da sadaukarwar da sojojin suka nuna ba, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Sadaukarwar da kwamandan rundunar, manyan jami'ai uku da sojoji 12 suka nuna a yayin wannan mummunan lamarin ba za a manta da ita ba.
"Jarumtarsu da jajircewarsu ya nuna tsantsar kishin ƙasa, ƙarfin gwiwa da sadaukarwa wanda za mu ci gaba da yin koyi da shi.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun halaka sojoji 22 a wani mummunan kwanton bauna

"Ina so in yaba da martanin gaggawa da babban hafsan hafsoshin tsaro ya ɗauka na ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa domin cafko waɗanda ke da alhakin wannan ɗanyen aikin.
"Yana da muhimmanci a tabbatar da adalci kuma a hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika."

Kisan soji 16: Gwamna Sheriff ya yi martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi tofin Allah tsine kan kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar.

Gwamnan ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalansu, inda ya ce gwamnati za ta bi duk hanyoyin da suka dace don ganin an hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel