Abdul Ningi: Akwai Yiwuwar Sanata Zai Koma Kujerarsa Amma da Sharadi, Akpabio Na Cikin Matsi

Abdul Ningi: Akwai Yiwuwar Sanata Zai Koma Kujerarsa Amma da Sharadi, Akpabio Na Cikin Matsi

  • Akwai yiwuwar Sanata Abdul Ningi zai koma kujerarsa bayan dakatar da shi da aka yi a Majalisa Dattawa
  • Wata majiya daga Majalisar ta tabbatar da cewa yanzu haka ana sasatawa domin ganin Ningi ya dawo kujerarsa
  • Wannan na zuwa ne bayan dakatar da sanatan har na tsawon watanni uku kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar janye matakin dakatarwa kan Sanata Abdul Ningi da aka yi.

Majalisar Dattawa ta dakatar da sanatan ne kan zargin cushe na tiriliyan 3.7 kasafin kudin shekarar 2024.

An kan tattaunawa kan makomar Abdul Ningi bayan dakatar da shi
Sanata Abdul Ningi zai iya komawa kujerarsa yayin da ake neman maslaha. Hoto: Abdul Ahmed Ningi, The Nigeria Senate.
Asali: Facebook

Menene rahotanni ke cewa kan Ningi?

Kara karanta wannan

Malaman jami'a karkashin SSANU za su shiga yajin aiki, sun fadi yaushe za su dawo

Wata majiya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ta ce an yi zargin cushen ne domin batawa Majalisar suna a idon duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce amma yanzu haka ana kokarin kawo karshen lamarin cikin ruwan sanyi, cewar Leadership.

Sanatan da ya bukaci a boye sunansa ya ce nan ba da jimawa ba za a iya mayar da Ningi kujerarsa amma da sharadin zai ba da hakuri ga Majalisar.

"Zan iya fada muku cewa babu wata matsala a Majalisar, zargin cushe a kasafin kudi yunkuri ne na batawa Majalisar suna."
"Ana ƙoƙarin batawa Majalisar suna saboda Godswill Akpabio wanda kullum kokari ya ke ya ga an samu daidaito tsakanin majalisar da bangaren zartarwa."

- Cewar majiyar

Dalilin dakatar da Sanata Abdul Ningi

Wannan na zuwa ne bayan dakatar da sanatan har na tsawon watanni uku kan zargin cushe da ya yi a kasafin kudin.

Kara karanta wannan

Dakatar da Sanata Ningi ya haifawa majalisar dattawa fushin kungiyoyin Arewa

Dakatarwar ta jawo kace-nace daga bangarori da dama a kasar inda aka yi kiran a yi gaggawar dawo da shi.

Gwamna Bala ya goyi bayan Sanata Ningi

Kun ji cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya nuna damuwa kan yadda aka dauki mataki kan Sanata Abdul Ningi.

Gwamnan ya ce su na goyon bayan sanatan musamman idan har a kan gaskiya ya ke saboda bin tsarin da ya dace

Hakan ya biyo bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa wanda dan asalin jihar Bauchi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel