Jerin Sanatoci 13 Na Majalisar Dattawa Ta 10 da Suka Taba Riƙe Muƙamin Gwamna

Jerin Sanatoci 13 Na Majalisar Dattawa Ta 10 da Suka Taba Riƙe Muƙamin Gwamna

  • Akalla tsofaffin gwamnoni 13 ne da a yanzu suka koma sanatoci a majalisar dattawa ta 10 biyo bayan babban zaben kasar na 2023
  • Duk da cewa babu wata doka a Najeriya da ta hana tsofaffin gwamnoni neman zama sanatoci, amma manazarta na ganin kamar sun mayar da abun al'ada
  • Yayin da tsarin mulki ya kayyade wa'adin mulki na shekaru takwas ga kujerar gwamna, ita kujerar sanata ba ta da wa'adi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsawon shekaru kenan majalisar tarayya ta zama abin da mutane da yawa ke kwatantawa a matsayin 'gidan ritayar tsofaffin gwamnoni.'

Duk da cewa babu wata doka a Najeriya da ta hana su neman zama sanatoci, amma manazarta na ganin cewa tsofaffin gwamnoni sun mayar da komawa majalisar dattawa kamar al'ada.

Kara karanta wannan

Matatar man Fatakwal za ta fara aiki yayin da Najeriya ke shirin daina shigo da fetur

Tsofaffin gwamnoni da suka koma sanatoci
Akwai tsofaffin gwamnoni 13 da yanzu suke zaune a majalisar dattawa ta 10. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Sabanin kujerar gwamna da tsarin mulki ya kayyade wa'adin mulki na shekaru takwas (shekaru hudu a kowanne wa'adi), Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa su sanatoci ba su da wa'adi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai sanatoci 109 a majalisar dattawan Najeriya. Kowace jiha daga jihohi 36 na tarayyar na da sanatoci uku yayin da sanata daya ya fito daga Abuja, babban birnin kasar.

Shafin kididdiga na StatiSense ya wallafa a X cewa akwai tsofaffin gwamnoni 13 da suka samu kujeru a majalisar dattawa ta 10 bayan gudanar da zaben 2023.

Tsoffin gwamnoni a majalisar dattawa ta 10

1. Abia: Orji Kalu

Duk da matsalolin da ya fuskanta kasancewarsa dan jam’iyyar adawa a Abia, jihar PDP ta lokacin, an sake zaben Sanata Orji Kalu a 2023 daga gundumar Abia ta Arewa.

Mista Kalu ya rike kujerar gwamnan jihar Abia na tsawon wa'adi biyu tsakanin watan Mayun 1999 zuwa watan Mayun 2007.

Kara karanta wannan

Tinubu na fuskantar sabuwar matsala yayin da 'yan fansho ke shirin fita zanga-zanga tsirara

Ya gaza samun wasu mukaman gwamnati bayan saukarsa daga gwamna har sai da ya koma APC a watan Nuwamban 2016.

2. Akwa Ibom: Godswill Akpabio

Mista Godswill Akpabio ya taba rike mukamin gwamnan jihar Akwa-Ibom na wa’adi biyu tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin jam’iyyar PDP.

Daga baya ya lashe kujerar sanata na Akwa-Ibom ta Arewa maso Yamma a karkashin jam’iyyar a shekarar 2015 lokacin da ya bar kujerar gwamnan jihar.

Mista Akpabio ya samu nasarar zama shugaban majalisar dattawa na majalisar ta 10 bayan samun goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu da jam'iyyar APC.

3. Bayelsa: Seriake Dickson

Seriake Dickson ya sake komawa majalisar dattawa a shekarar 2023 a karo na biyu. Wannan na zuwa bayan rike mukamin gwamnan Bayelsa daga 2012 zuwa 2020 a karkashin PDP.

An fara zaben shi a matsayin sanatan mazabar Bayelsa ta Yamma a watan Oktoba na 2020 a wani zaben cike gurbi da aka yi a shekarar.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamnan APC zai rage farashin kayan abinci da 25% yayin da aka fara azumi

4. Edo: Adams Oshiomole

Adams Oshiomhole dai tsohon gwamnan jihar Edo ne wanda ya yi wa'adi biyu yana mulki tsakanin shekarar 2008 zuwa 2016.

Oshiomole ya lashe zaben kujerar sanata mai wakiltar Edo ta Arewa a karon farko a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

5. Gombe: Danjuma Goje

Danjuma Goje ya kammala wa’adinsa na gwamnan jihar Gombe a shekarar 2011- bayan ya yi wa’adi biyu a jere daga 2003, a karkashin jam’iyyar PDP.

An fara zabarsa a matsayin sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a jam'iyyar PDP a shekarar 2011. A shekarar 2014 ya fice daga PDP zuwa APC, inda a karkashinta ya sake lashe zabensa na sanata a 2015, 2019 da 2023.

6. Gombe: Ibrahim Danwkambo

Ibrahim Danwkambo ya kasance gwamnan jihar Gombe har na wa'adi biyu daga 2011 zuwa 2019 a karkashin jam'iyyar PDP.

An zabi tsohon gwamnan a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar Gombe ta tsakiya a shekarar 2023, inda ya doke dan takarar jam’iyyar APC Seidu Akali.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

7. Kebbi: Adamu Aliero

Adamu Aliero ya kasance gwamnan jihar Kebbi tsakanin 1999 zuwa 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. Tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua ya nada Mista Aliero ministan Abuja a watan Disambar 2008.

Nasarar da Mista Aliero ya samu a zaben 2023 na kujerar dan majalisar dattawa ya sa ya sake komawa majalisar a karo na hudu.

8. Neja: Abubakar Bello

Shafin Wikipedia ya wallafa cewa Abubakar Sani Bello, wanda aka fi sani da Lolo, dan siyasan Najeriya ne wanda a yanzu ya ke matsayin sanata mai wakiltar Neja ta Arewa.

Ya taba zama gwamnan jihar Neja daga 2015 zuwa 2023, kuma shi mamba ne a jam'iyyar All Progressives Congress.

9. Ogun: Gbenga Daniel

Mista Daniel ya kasance gwamnan jihar Ogun a na tsawon shekaru takwas. Ya yi mulki tsakanin 2003 zuwa 2011 a jam'iyyar PDP.

A watan Fabrairun 2021, Daniel ya koma APC daga PDP inda ya lashe kujerar Sanatan Ogun ta Gabas a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a kasuwar Wuse, babban birnin tarayya Abuja, ta yi barna

10. Plateau: Simon Lalong

Shafin Wikipedia ya wallafa cewa Simon Bako Lalong CON lauyan Najeriya ne kuma dan siyasa wanda yanzu ya ke a majalisar dattawa daga mazabar Filato ta Kudu, bayan lashe zaben kujerar a 2023.

Ya taba rike mukamin ministan kwadago da ayyuka a shekarar 2023, sannan kuma ya yi gwamnan jihar Filato daga shekarar 2015 zuwa 2023.

11. Sokoto: Aliyu Wammako

Mista Wammako, wanda ya taba zama gwamnan jihar Sokoto a karo na biyu, ya rike mukamin ne tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015.

A 2023, tsohon gwamnan ya sake zama Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa karkashin APC. An fara zabar shi a matsayin sanata a 2015 kuma ya sake lashe zaben a 2019.

Karashen sunayen na zuwa...

Gwamnonin da suka rasa kujerun sanatoci

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo bayani kan wasu gwamnonin Najeriya shida da suka gaza cin zaben kujerar majalisar dattawa a 2023.

Duk da cewa suna da madafun iko a hannunsu, amma hakan bai hana 'sa'a' ta juya masu baya ba, inda suka yi abun da Bahaushe ke kira "ba uwa ba riba".

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.