Bayan Ningi Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabon Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa

Bayan Ningi Ya Yi Murabus, An Naɗa Sabon Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa

  • Kungiyar sanatocin Arewa (NSF) ta naɗa Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdul'aziz Yar'adua a matsayin sabon shugabanta bayan Abdul Ningi ya yi murabus
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da haka a zaman majalisa na ranar Alhamis, 14 ga watan Maris
  • Sanata Ningi ya yi murabus daga kujerar shugaban NSF ne bayan majalisar dattawa ta dakatar da shi na tsawon watanni uku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanata Abdulaziz Musa Yar’Adua (APC, Katsina ta Tsakiya), a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024 ya zama sabon shugaban kungiyar Sanatocin Arewa (NSF).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohon shugaban kungiyar, Sanata Abdul Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya ya yi murabus daga mukamin ranar Talata.

Kara karanta wannan

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, fitaccen Sarki Mai Martaba a Najeriya ya rasu a watan Ramadan

Sanata Abdul'azin Musa Yar'adua.
Yar’Adua Ya Maye Gurbin Ningi a Matsayin Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa Hoto: Abdulaziz Musa Yar'adua
Asali: Facebook

Meyasa Sanata Abdul Ningi ya yi murabus?

Sanata Ningi ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan dakatarwar da majalisar dattawan Najeriya ta masa na tsawon watanni uku, Channels tv ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta dakatar da Ningi ne saboda ikirarin karya da ya yi cewa an yi wa kasafin kuɗin 2024 cushen makudan kudi har Naira tiriliyan 3.7.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Solomon Adeola, ya yi bayani kan kuɗin da Ningi ya yi tunanin cewa cusa su aka yi a kasafin kuɗin.

Adeola ya ce kuɗin da Sanata Ningi ya kira da cushe an ware su ne ga wasu hukumomin gwamnati kai tsaye kamar yadda doka ta tanada.

Sanatoci sun naɗa sabon shugaban NSF

Ƙungiyar sanatocin Arewa NSF ta rubuta wasiƙa tare da aika ta zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kan sauyin da aka samu.

Kara karanta wannan

Cushen N3.7trn: Shugaban majalisar dattawa zai yi murabus saboda kalaman PDP? An bayyana gaskiya

Sanata Akpabio ya karanta wasiƙar a zaman ranar Alhamis, inda ya ayyana Sanata Yar'adua daga jihar Katsina a matsayin sabon shugaban sanatocin Arewacin Najeriya.

Abdul'aziz Ƴar'adua ya fito ne daga jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya kuma yana wakiltar mazaɓar Katsina ta tsakiya a majalisar dattawa ta 10.

Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa APC?

A wani rahoton na daban Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙara jaddada cewa har yanzu shi 'dan jam'iyyar PDP ne duk da ƙoƙarin wasu jiga-jigai na ganin an kore shi.

Tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana haka ne yayin hira da wasu zaɓaɓɓun yan jarida a Abuja, ya ce babu abin da ya canza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel