Ministan Tinubu da CP Sun Sa Labule da Sanatoci a Zauren Majalisar Tarayya, Bayanai Sun Fito

Ministan Tinubu da CP Sun Sa Labule da Sanatoci a Zauren Majalisar Tarayya, Bayanai Sun Fito

  • Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri ta ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan tabarɓarewar tsaro wanda ya fara shigowa kwaryar birnin
  • Wike tare da kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igwe, sun amsa gayyatar da majalisar ta aika masu a makonnin da suka shige
  • Wannan taro na zuwa ne bayan wani farmakin garkuwa da mutane da ƴan bindiga suka kai Anguwar Galadima a cikin birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, yana ganawa yanzu haka da sanatoci a zauren majalisar tarayya yau Laraba, 13 ga watan Maris.

Wannan taron ya samo asali ne daga yanayin taɓarɓarewar tsaro a birnin tarayya Abuja a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi kudin fansan da gwamnatinsa za ta biya don ceto daliban da aka sace a Kaduna

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rashin tsaro: Ministan Abuja ya amsa gayyatar majalisar dattawa Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa taron na sirri yana gudana ne a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sha fama da jerin hare-haren garkuwa da mutane a garuruwan birnin Abuja a ƴan makonnin nan, inda mutane ke biyan maƙudan kuɗin fansa.

Lamarin dai ya lalace ta yadda idan har dangi ba su biya kuɗin da masu garkuwa suka nema ba, za su iya shiga haɗarin yiwuwar rasa ƴan uwansu.

Menene maƙasudin kiran wannan taron a majalisa?

A rahoton Channels tv, majalisar dattawa ta shiga taron sirri da Wike ne tare da kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igwe.

Majalisar ta gayyaci minista da kwamishina domin su mata ƙarin haske kan yanayin tsaron Abuja musamman bayan harin garkuwa da mutane da ya auku a anguwar Galadima da ke cikin birni.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama hatsabiban masu garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a Arewa

Ana sa ran a wannan zama, Wike da kwamishinan ‘yan sanda za su yi ƙarin haske game da yanayi tsaro da matakan da suke ɗauka a babban birnin tarayya.

Gwamna Bago ya amince da ƙarin albashin ma'aikata

A wani rahoton na daban kuma awanni bayan kalaman Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Umar Bago ya amince da biyan N20,000 a matsayin kyautar albashi ga ma'aikatan jihar Neja.

Yayin ziyarar da ya kai Minna, Shugaba Tinubu ya roki gwamnoni su fara biyan kyautar albashi domin rage raɗaɗin da mutane ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel