Okuama: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Faɗi Waɗanda Yake Tunanin Suna da Hannu a Kisan Sojoji 17

Okuama: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Faɗi Waɗanda Yake Tunanin Suna da Hannu a Kisan Sojoji 17

  • Sanata Godswill Akpabio ya ce ba ya tunanin ƴan yankin Neja Delta ne suka kashe dakarun sojoji 17 a Okuama, jihar Delta
  • Shugaban majalisar dattawa ya ce mai yiwuwa wasu ƴan ƙasar waje ne suka shigo suka aikata wannan ɗanyen aiki
  • Majalisar ta umarci gwamnati ta kamo duk masu hannu domin su girbi abin da suka shuka, kana ta yi shirun minti ɗaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce mai yiwuwa masu hannu a kisan sojojin Najeriya 17 a jihar Delta duk ƴan kasar waje ne.

Idan ba ku manta ba wasu matasa ɗauke da makamai sun kai farmaki tare da kashe sojoji 17 da suka je aikin wanzar da zaman lafiya a Okuama, ƙaramar hukumar Ughelli.

Kara karanta wannan

Okuama: Bola Tinubu ya gana da gwamnan PDP kan kisan sojoji 17, sahihan bayanai sun fito

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio.
"Ta yiwu waɗanda suka kashe sojoji 16 ba ƴan Najeriya bane" Akpabio Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis, 14 ga watan Maris 2024 a jihar Delta da ke yankin Neja Delta, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya faɗi waɗanda yake zargi

Da yake jawabi yayin muhawara kan wasu kudirori biyu da aka cure wuri ɗaya, Sanata Akpabio ya ce yana zaton waɗanda suka kashe sojojin ba ƴan Najeriya ba ne.

Sanata Abdulaziz Yar’Adua (APC, Katsina ta Tsakiya) da Sanata Edeh Dafinone (APC, Delta ta Tsakiya) ne suka kai kudirorin guda biyu kan wannan kisan gilla.

Yayin da yake faɗin ra'ayinsa kan lamarin da ya faru, shugaban majalisar dattawa ya ce:

"Ba cikin yaƙi muke ba, ba na tunanin (waɗanda suka kashe sojojin nan) ƴan yankin Neja Delta ne, ta yiwu sojojin haya ne daga wata ƙasar."

Wane matakai majalisar dattawa ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Kisan sojoji 16: Majalisar dattawa ta yi martani kan harin, ta fadi matakin dauka

Daga nan sai majalisar dattawan ta ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan kisan gillan da aka yi wa dakarun sojojin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ta bukaci kwamitinta na tsaro, sojin ƙasa, sojin ruwa, da sojin sama da su tuntubi hukumomin sojoji don samun karin bayani kan ainihin abin da ya haddasa lamarin wanda ta kira da 'mummunan aiki'

Majalisar ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika kana ta kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Bayan haka kuma majalisar dattawa ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama waɗanda aka kashe.

Okuama: Tinubu ya gana da gwamnan Delta

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Delta a fadar shugaban kasa kan mummunan lamarin da ya yi ajalin sojoji.

Jim kaɗan bayan ganawarsu, Gwamna Oborevwori ya tabbatar da cewa duk mai hannu a kisan gillan da aka yi wa sojojin zai ɗanɗana kuɗarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel