Hukumar NEMA
Bayan sa bakin Minista Pantami MTN sun hakura da kara farashin USSD. MTN sun fadi abin da ya sa su ka hakura da kara kudin USSD a makon jiya. Tuni dai har gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele ya yi magana kan batun.
Babban bankin CBN sun kawo sabon tsarin karbar kudi daga masu adana manyan kudi inda za a rika karbar kashi 2% zuwa 5% idan aka yi babban ajiya. Kuma masu cirr kudi daga banki za su rika biyan wani kason.
Mun samu labari cewa Legas da Jihohin da ke makwabtaka da ita za su gamu da ambaliya. Hukumar bada agajin ta sanar da gwamnatocin jihohin da abin zai shafa cewa su shirya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai sanadiyar tsawa a ranar Alhamis a Yola. Mista Abani Garki, shugaban kula da ayyukan hukumar a jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana hakan.
Duk da uwar yunwa da ake tafkawa a sansanonin masu gudun hijira da yakin Boko Haram ko na makiyaya ya rutsa dasu, ashe ana jibge da shinkafa a suto-suto na hukumar NEMA, hukuma da aka kafa don kawo daukin gaggawa ga wadanda bala'i
Rahotanni sun kawo cewa tun da aka shiga kakar ruwan saman bana, guguwar iska ta rusa gidaje 1000 a jihar Kebbi da Zamfara, inji hukumar bada agajin gaggawa.
Hukumar NEMA
Samu kari