USDD: Bayan sa bakin Minista da NCC, MTN sun hakura da karin kudi

USDD: Bayan sa bakin Minista da NCC, MTN sun hakura da karin kudi

Kawo yanzu kamfanin sadarwan MTN ba su kara kudin hawa shafin USSD kamar yadda su ka sanar a baya ba cewa za a rika cire N4 a kan kowane dakila 20 da aka yi a kan shafin.

MTN Nigeria ta sanar da cewa ba ta fara dabbaka wannan sabon tsarin farashi ba tukuna. A cewar kamfanin, ta janye wannan shiri na ta ne bayan gwamatin kasar ta shigo cikin maganar.

Kafar USSD watau "Unstructured Supplementary Service Data" ya kan ba masu amfani da kafafen sadarwar damar hawa shafukan bankinsu domin aika kudi ko kuma yin wasu abubuwan.

Wani babban jami’in hulda da mutane na kamfanin MTN, Mista Funso Aina, ya bayana cewa ba su kara kudin USSD ba tukuna bayan sun bada sanarwar yin hakan a Ranar Lahadi da ta gabata.

KU KARANTA: An ba Buhari shawara game da MTN da sauran kamfanonin Afrika ta Kudu

Funso Aina ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi magana a madadin kamfanin sadarwar kasar Afrika ta Kudun da wani ‘dan jaridar Daily Trust a Ranar Litinin 21 ga Watan Oktoba.

Aina ya bayyana cewa sun tsaida da shirin ne bayan wani umarni da ya fito daga hukumar sadarwar Najeriya na NCC a Ranar Lahadin na cewa kamfanin su dakatar da shirin.

Ministan sadarwan Najeriya Dr. Isa Ali Pantami shi ne ya umarci hukumar NCC ta tsaida yunkurin da MTN ta ke yi ba tare da sanar da hukuma ba, bayan jama’a sun jawo hankalinsa.

Shi ma dai gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi magana a game da shirin lokacin da yake halartar wani taro a Amurka inda ya nemi bankuna su dauki mataki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel