Za a kwarara ambaliya a Legas da Jihohin kewaye Inji NEMA

Za a kwarara ambaliya a Legas da Jihohin kewaye Inji NEMA

Labari ya zo mana cewa hukumar da ke bada agajin gaggawa a Najeriya watau NEMA, ta yi gargadi cewa za a cigaba da fuskantar ambaliyar ruwa a jihohin Legas da kewayenta kwanan nan.

NEMA ta bada wannan gargadi ne ta bakin Jami’in da ke magana da yawun bakinta, Ibrahim Farinloye. Hukumar ta ce jama’a su sa ran cewa za a sheka ruwa a watan Satumban gobe.

Hukumar ta yi wannan bayani ne a Ranar Lahadi, 11 ga Watan Agusta, 2019 a Garin Abeokuta da ke cikin Jihar Ogun. Farinloye ya yi wannan jawabi ne a wajen wani taron da NEMA ta shirya.

Mista Farinloye ya ke cewa binciken da su ka yi ya nuna masu za a yi ambaliya a Legas da jihohin da ke makwabtaka da ita a cikin shekarar nan. Sakacin hukuma ne zai jawo wannan ambaliya.

KU KARANTA: A na binciken abin da ya sa wuta ta ci wasu Yara a Legas

Za a samu wannan matsala ne saboda rashin hanyoyin ruwa a cikin Birane da Kauyukan jihohin Kudu maso Yammacin kasar inji Farinloye wanda ya ce tuni sun sanar da gwamnoni wannan.

Hukumar bada agajin ta aikawa gwamnatocin jihohin da abin zai shafa takarda domin su yi tanadi. NEMA ta daura laifin ne kan jihohi da kananan hukumomi da ba su gina hanyar ruwa.

Jami’in ya ce: “Ku je Legas, za ku ga yadda a ka cika hanyoyin ruwa da dattin bola da tarkace.” Darekta Janar (na NEMA) ya aikawa gwamnoni takarda ya na jan hankalinsu. Inji Farinloye.

An kuma ja hankalin masu tuka babura su bi a hankali da tituna a wannan lokaci na damina. Wani babban Jami’in hukumar NEMA, Aliyu Waziri, ya yabawa gwamnatin tarayya a wajen taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel