Shugaban NEMA na yankin arewa maso gabas ya mutu a Borno

Shugaban NEMA na yankin arewa maso gabas ya mutu a Borno

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta sanar da mutuwar Saidu Ahmed, shugabanta na yankin arewa maso gabas.

Abdulkadir Ibrahim, shugaban sashen yada labarai na NEMA a yankin arewa maso gabas, ne sanar da mutuwar Ahmed yayin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ibrahim ya ce shugaban ya mutu ne ya asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri (UMTH) bayan ya sha fama da ciwon sukari.

"Har yanzu mu na asibitin domin daukan gawarsa," a cewar Ibrahim.

Ya yi addu'ar Allah ya yafe kura-kuran marigayin tare da bawa iyalinsa hakurin jure rashinsa.

Kazalika, dan majalisar Borno mai wakiltar mazabar Bayo a majalisar jihar, Umar Audi ya rasu.

Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Maiduguri a yammacin ranar Talata kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

An ce ma'aikatan lafiya a asibitin sun dage cewa babu gadon da za a bashi inda suka ce gadon kawai da ya rage na mata masu haihuwa ne.

Amma iyalansa da suka kai shi asibitin sun yi nasarar shawo kan ma'aikatan asibitin, inda daga bisani suka karbe shi.

Shugaban NEMA na yankin arewa maso gabas ya mutu a Borno
Shugaban NEMA na yankin arewa maso gabas ya mutu a Borno
Asali: UGC

Majiyar ta ce, "ya mutu jim kadan bayan an bashi gado. An dauki samfuri daga jikinsa an aike wa Hukumar kiyayye cututtuka masu yaduwa, NCDC, domin a tabbatar idan mutuwarsa na da alaka da COVID-19.”

A jihar Katsina, an kwantar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar a sashen kula na musamman (ICU) na asibitin tarayya da ke jihar Katsina.

DUBA WANNAN: Barnar Abacha: Yadda gwamnatin Buhari za ta kashe $311m da Amurka ta dawo da su - Fadar shugaban kasa

Wata majiya daga fada a ranar Talata ta ce an gaggauta mika Umar asibiti a daren Litinin kuma an kwantar da shi sakamakon mawuyacin halin da yake ciki.

Ana zargin Umar ya kwashi cutar COVID-19 daga likitan nan na jihar Katsina, Dr Aminu Yakubu, wanda ya rasu sakamakon cutar a watan da ya gabata.

SaharaReporters ta gano cewa marigayi Yakubu ne likitan mai martaba sarkin Daura Umar Farouk da matarshi, Hajiya Binta Umar, wacce ta mutu a cikin watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel