CBN za ta rika karbar kashi 2% zuwa 5% idan aka yi babban ajiya ko diba

CBN za ta rika karbar kashi 2% zuwa 5% idan aka yi babban ajiya ko diba

- CBN sun kawo sabon tsarin karbar kudi kan masu yin manyan ajiya a banki

- Haka zalika wadanda za su ciri kudi daga banki za su rika biyan wani abu

- Wannan tsari zai fara aiki jihohi irin su Legas, Ogun, Kano, da kuma Abuja

Babban bankin Najeriya na CBN ya bada sanarwar cewa bankunan da ke karbar ajiya za su rika cire wani kaso na kudin da su ka adanawa jama’a. An bada wannan sanarwa ne a jiya Latata.

An kawo wannan tsari ne domin a rage yawo da tsabar kudi a fadin kasar. Bankunan da ke adana kudin mutane watau DMB za su rika karbar wani kaso idan mutum zai zare kudi ko zai ajiye.

A jawabin da CBN ta fitar jiya, 16 ga Watan Satumba, 2019, daga yau za a rika karbar kashi 3% na kudin mutum idan zai cire abin da ya kai N500, 000 daga banki domin hana yawo da tsabar kudi.

KU KARANTA: Buhari ya na ta samun yabon Masana bayan ya jawo Masana tattali

CBN za ta rika karbar kashi 2% zuwa 5% idan aka yi babban ajiya ko diba
Daga yau za a fara karbar kamasho daga masu adana manyan kudi
Asali: UGC

Haka zalika banki za su tashi da kashi 2% na kudin da mutun ya adana muddin kudin ya kai N500, 000. Wannan zai fara aiki ne a Legas, Ogun, Kano, Abia, Anambra, Ribas da kuma birnin tarayya Abuja.

Hukuma ta kirkiro wannan tsarin karbar kudin aiki ne a kan tsarin da ake da shi a kasa wajen domin ganin an cin ma dogon burin nan na farkon shekarar 2020 inda ake so a daina yawo da takardun kudi.

Za a rika zaftare 5% ne idan masu kamfani su ka zo cire tsabar kudi daga banki, kuma za a rika karbar 3% daga hannun su a duk lokacin da su ka kawo kudinsu domin a zuba masu cikin akawun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng