Shinkafar da China ta aiko wa 'yan gudun hijira ta rube a suto din NEMA, bayan sunki rabarwa (Hotuna)
- Kasar China ta aiko agajin shinkaffa jirgin ruwa guda
- An ajje shin kafar an ki rabawa jama'a har ta rube
- Ana yunwa a sansanonin gudun hijira
Duk da uwar yunwa da ake tafkawa a sansanonin masu gudun hijira da yakin Boko Haram ko na makiyaya ya rutsa dasu, ashe ana jibge da shinkafa a suto-suto na hukumar NEMA, hukuma da aka kafa don kawo daukin gaggawa ga wadanda bala'i ya abkawa.
Kasar Chena ce dai ta aiko agajin, amma bai isa inda ya kamata ba har aka barshi ya lalace, bayan kuma akwai mabukata a ko'ina a fadin kasar nan.
DUBA WANNAN: An saki bidiyo da ba lallai yayi wa Buhari ko APC dadi ba
A baya ma an sha kama kayan agajin ana sayarwa a kasuwa, an sace daga hannun hukumar ko an canja akalar kayan bayan anyi kiliyarin dinsu.
Ana kuma tuhumar babban cin hanci a hukumar karkashin wasu daraktocinta a EFCC.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng