Hukumar NERC za ta yi wani zama na biyu a kan farashin wutar lantarki
- NERC za ta sake duba farashin wuta ganin ana shirin shiga sabuwar shekara
- Duk shekara Gwamnati za ta iya yin kari ko kuma ragi a kan kudin shan wuta
- Ana yin la’akari da wasu abubuwa kafin hukumar NERC ta tsaida kudin wuta
Hukumar NERC mai sa ido a harkar wutar lantarki a Najeriya, ta sanar da jama’a game da zaman da za ayi domin duba farashin shan wuta a kasar.
Daily Trust ta rahoto cewa NERC za ta yi wannan zama karo na biyu kenan a shekarar nan ta 2020.
Ana sa ran hukumar ta karbi bayanai da gudumuwar jama’a nan da makonni uku kamar yadda jaridar ta bayyana a ranar 26 ga watan Nuwamba.
KU KARANTA: Kamfanonin DisCos sun kara farashin kudin wuta
A wani jawabi da NERC ta fitar tun a ranar Laraba, ta ce hukuma za ta duba farashin kamfanoni masu harkar wura irinsu DisCos, GenCos da TCN.
Wadannan kamfanoni sune ke da alhakin bada wa, jawo wa da kuma raba wutar lantarki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NERC mai shirin barin-gado, Farfesa James Momoh ba zai jagoranci wannan zama da za ayi a karshen shekara ba, a makon nan zai bar ofis.
A shekarar nan ta 2020 ne aka shigo da sabon farashin shan wuta inda mafi yawan jama’a suka fuskanci karin fiye da 50% na abin da suke biya a da.
KU KARANTA: Gwamnati ta dakatar da karin kudin wuta - Minista
Sabon tsarin kudin wutan na 2020 ya fara aiki ne a watan Nuwamba, kuma za ayi aiki da wannan tsarin farashi har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
Gwamnati za ta iya shigo da sabon tsari daga watan Junairun 2021, ana amfani da darajar dala, farashin gas, tsadar kaya wajen kari ko rage kudin wutan.
Kwanakin baya kun ji cewa Ministan wutar lantarki na Najeriya, Injiniya Saleh Mamman ya ce nan ba da dadewa ba, 'yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari.
Ministan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, wajen kokarin bayyana cigaban da aka samu a fannin wutar lantarki a wannan gwamnati mai-ci ta APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng