Bayan Rasa Takara a APC, Sanata Goje Ya Magantu kan Makomar Siyasarsa

Bayan Rasa Takara a APC, Sanata Goje Ya Magantu kan Makomar Siyasarsa

  • Sanata Muhammad Danjuma Goje ya yi magana kan makomar siyasarsa bayan rasa tikitin takarar sanata karkashin APC
  • Goje ya musanta ficewa daga APC, yana mai cewa har yanzu ɗan jam’iyyar ne, amma zai bayyana matakinsa na gaba nan gaba
  • Tsohon gwamnan Gombe ya ce ya yi nasara a dukkan zaɓukan takara takwas da ya shiga, yayin da ya tabbatar da ci gaba da tallafa wa jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Tsohon gwamnan Gombe kuma Sanatan Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya yi magana kan siyasarsa.

Sanata Goje wanda kuma ya taba jagorantar jihar Gombe a matsayin gwamna ya ce har yanzu yana tuntubar mutane kan makomar siyasarsa.

Goje ya tabbatar da shirin yanke hukunci kan makomar siyasarsa
Sanata Muhammad Danjuma Goje daga jihar Gombe. Hoto: Muhammad Adamu Yayari.
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa shugabannin jam’iyyun PDP da APC suna matsa wa Sanata Goje lamba domin ya koma jam’iyyunsu, bayan jam'iyya mai mulki ya ta hana shi tikitin takara ba.

Kara karanta wannan

Shin da gaske Sanata Danjuma Goje ya fice daga jam'iyyar APC?

Goje ya magantu kan makomar siyasarsa

Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, Goje ya musanta cewa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya, yana mai tabbatar da cewa har yanzu yana cikin APC.

Ya ce:

“Har yanzu ina APC ban koma wata jam'iyya ba, amma nan da lokaci kadan zan bayyana makomar siyasa ta, ina bukatar ku da ku ci gaba da ba da shugabannin jam'iyya hadin kai da goyon baya."

Sanatan, wanda ke wa’adinsa na huɗu a Majalisar Dattawa, ya bukaci magoya bayansa su koma yankunansu tare da jiran ƙarin bayani daga gare shi.

Goje ya waiwayi kusan shekaru 45 da ya shafe yana siyasa, inda ya ce ya tsaya takara sau takwas tun daga Jamhuriya ta Biyu zuwa yanzu, kuma ya yi nasara a dukkan zaɓukan.

Goje ya musanta barin APC
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje. Hoto: Muhammad Adamu Yayari.
Source: Twitter

Yadda mutane ke son Goje ya yi takara

A cewarsa, ya amince da matsin lambar magoya bayansa ya sake tsayawa takara a 2023, bayan da ya sanar tun 2019 cewa zai yi ritaya daga siyasa kuma ba zai shiga zaɓen 2023 ba.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC Salihu Mustapha ya yi watsi da jam'iyyar, ya yi murabus

Goje ya kasance yana wakiltar mazabar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa tun 2011, bayan ya kammala wa’adinsa biyu a matsayin gwamnan Gombe, cewar Punch.

Sai dai yunkurinsa na komawa Majalisar Dattawa karo na biyar ya samu koma baya, bayan da bai yi nasara a zaɓen fidda gwani kai tsaye na APC ba.

Kwamitin zaɓen fidda gwani na APC na Gombe ya ayyana DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya) a matsayin ɗan takarar jam’iyyar na kujerar Sanatan Gombe ta Tsakiya.

INEC ta fitar da sunaye babu na Goje

A baya, an ji cewa Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takarar zaɓen 2027 na ƙarshe, inda aka rasa sunan tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Fitattun sanatoci a Najeriya sun rasa sunayensu a cikin jerin takardun ƙarshe da INEC ta fitar wanda ke kara tabbatar da cewa sun damar tsayawa takara a 2027.

Duk da APC ta mayar da sanatoci shida bayan duba ƙorafe-ƙorafe, wasu fitattun 'yan siyasa sun ci gaba da kasancewa a wajen jerin sunayen ƙarshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.