Akwai Kura: Shugaban Iran Ya Bayyana Matsalolin da Suka Addabi Kasar

Akwai Kura: Shugaban Iran Ya Bayyana Matsalolin da Suka Addabi Kasar

  • Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce al’ummar kasar na fuskantar matsaloli da dama, musamman na tattalin arziki da rayuwa
  • Amurka ta kara kakaba wa Iran sababbin takunkuman tattalin arziki da nufin kara ware tattalin arzikin kasar
  • Pezeshkian ya ce gwamnatinsa na kokarin magance hauhawar farashi, rashin aikin yi da matsalolin rayuwa domin al’umma su samu damar rayuwa cikin mutunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya amince cewa al’ummar kasar na fuskantar “matsaloli da dama”.

Masoud Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin da Amurka ke kara tsaurara takunkuman tattalin arziki da nufin kara matsa wa gwamnatin Tehran lamba.

Shugaban Iran ya yi maganganu
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: @drpezeshkian
Source: Twitter

Tashar Aljazeera ta ce Pezeshkian ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026 a wani jawabi da gidan talabijin na kasar ya watsa.

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Abin da Gwamna Radda zai yi kamfen da shi a Katsina

Shugaban kasar na Iran ya ce gwamnatinsa na kokarin rage matsalolin da al’umma ke fuskanta.

Amurka ta kara takunkumi kan Iran

Jawabin shugaban Iran ya zo ne bayan Amurka ta sanar da wani sabon zagaye na takunkumi kan tattalin arziki da nufin kara ware tattalin arzikin Iran.

A makon da ya gabata, Amurka ta kuma bayyana kudirinta na yin amfani da sababbin takunkuman wajen haifar da rugujewar gwamnatin Iran.

Pezeshkian ya ce saboda matakan da Shugaban Amurka Donald Trump ke dauka, Iran na fuskantar wani yanayi da ya kira cikakkiyar yakin tattalin arziki, soja da tsaro.

Ya ce Amurka na kokarin kakaba wa Iran takunkuman da za su yi matukar illa ga tattalin arzikin kasar.

Matsalolin tattalin arziki sun kara tsananta

Gwamnatin Iran ta fuskanci zanga-zangar jama’a sau da dama a shekarun baya, inda matsalolin tattalin arziki suka kasance daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa bore.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump ta ki tsorata Iran, jamhuriyar musulunci ta yi martani mai zafi

Hauhawar farashin kayayyaki da sauye-sauyen darajar kudin kasar sun rage karfin jama'a na sayen kayayyaki, lamarin da ya kara matsin rayuwa ga al’ummar Iran.

A karshen watan Disambar bara, wata zanga-zanga da ta fara sakamakon tsadar rayuwa ta rikide zuwa manyan zanga-zangar nuna rashin amincewa da shugabannin kasar.

Mahukuntan Iran sun ce sama da mutane 3,000 ne suka mutu a lokacin rikicin, tare da zargin Amurka da Isra’ila da hannu wajen haddasa tashin hankalin.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ke wajen Iran sun zargi hukumomin kasar da yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar, wanda suka ce ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Pezeshkian ya yi magana kan Iran
Masoud Pezeshkian, shugaban kasar Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Pezeshkian ya yi alkawarin magance matsalolin jama’a

Pezeshkian ya ce gwamnatinsa na yin iya kokarinta wajen magance matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da ke addabar al’ummar kasar.

Ya ce gwamnati na kokarin rage hauhawar farashi, matsalolin rayuwa da rashin aikin yi, tare da samar da kyakkyawar makoma ga al’umma.

Shugaban kasar ya kara da cewa burin gwamnatinsa shi ne tabbatar da cewa al’ummar Iran za su samu damar rayuwa cikin mutunci da alfahari.

Kara karanta wannan

Zargin safarar kwayoyi: Tinubu ya roki kotun Amurka kan shirin sake bayanansa

Iran ta yi wa Amurka martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da shirin Shugaban Amurka Donald Trump na kakaba wa Tehran wani sabon takunkumi kan tattalin arziki.

Abbas Araghchi ya bayyana cewa hakan ci gaba ne da “manufofin da suka gaza” da za su jawo wa Washington karin shan kaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng