Buratai Ya Kare Tinubu kan Zargin Safarar Kwaya, Ya Shawarci Yan Najeriya
- Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da tsoma bakin ƙasashen waje
- Buratai ya ce zarge-zargen da suka shafi Shugaba Bola Tinubu tun shekaru 33 da suka wuce bai kamata su ayyana makomar Najeriya ba
- Ya kuma bukaci shugabannin siyasa su haɗa kai, yana gargadin cewa sakin takardun binciken na iya cutar da tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da tsoma bakin ƙasashen waje cikin harkokin cikin gida.
Kiran na Buratai ya zo ne yayin da ake samun sababbin yunƙuri a Amurka na fitar da wasu takardun bincike da suka shafi Shugaba Bola Tinubu tun sama da shekaru 30 da suka wuce.

Source: Twitter
Buratai ya bayyana matsayinsa ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi 23 ga watan Agustan 2026.
Yadda martabar Najeriya ke zube wa
Tsohon janar ɗin ya ce wannan cece-ku-ce na iya lalata martabar Najeriya a idon duniya, musamman idan aka ci gaba da alakanta shugaban ƙasar da zarge-zargen da suka samo asali tun shekaru da dama.
Wata kotun tarayya da ke Washington, D.C., ta sanya ranar 28 ga Agusta, 2026 a matsayin wa’adin da Shugaba Tinubu, FBI da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka za su yi adawa da fitar da takardun.
Buratai ya yi gargadin cewa batun bai shafi Shugaba Tinubu kaɗai ba, yana mai cewa fitar da takardun na iya shafar mutunci, martaba da damar tattalin arzikin ’yan Najeriya miliyan 250.
Ya ce idan kafofin yaɗa labarai na ƙasashen duniya suka danganta shugaban da zarge-zargen safarar miyagun ƙwayoyi, duniya na iya kallon lamarin a matsayin matsala ta Najeriya baki ɗaya.
Zarge-zargen da suka gabata da martabar ƙasa
Buratai ya ce zarge-zargen da suka faru shekaru 33 da suka wuce ya kamata a bar su a baya, maimakon su ci gaba da bayyana tarihin Tinubu.
Ya bayyana cewa tsofaffin bayanai bai kamata su ayyana dogon tarihin Tinubu a siyasa ba, ciki har da zamaninsa a matsayin gwamnan Lagos da sauran ayyukansa na ƙasa.
Tsohon Shugaban Sojin ya kuma tambayi dalilin da ya sa kotun Amurka za ta tantance shugaban Najeriya mai ci, yana mai cewa ’yan Najeriya ne suka zaɓe shi.
Buratai ya ce kotunan Najeriya da hukumomin dimokuraɗiyya na cikin gida ne ya kamata su riƙe jami’an ƙasar da alhaki idan akwai bukatar hakan.
Ya bukaci shugabannin siyasa daga dukkan jam’iyyu su haɗa kai tare da sanya muradun Najeriya a gaba, yana gargadin cewa rikicin siyasa kan batun na iya cutar da tattalin arziki.
A cewarsa, mummunan labari daga ƙasashen duniya na iya tsoratar da masu zuba jari, tare da rage kasuwanci, kuɗaɗen da ’yan ƙasashen waje ke turawa gida da yawon buɗe ido.
Ya kuma yi gargadin cewa wasu ƙasashen waje na iya amfani da takardun wajen yin tasiri kan zaɓen shugaban ƙasa da sauran zaɓukan 2027.
Duk da cewa ya amince shugabanni dole su kasance masu ɗaukar alhaki, Buratai ya bukaci gwamnatin tarayya ta bi hanyoyin diflomasiyya wajen magance matsalar.
Ya shawarci tawagar lauyoyin Tinubu da su ƙalubalanci fitar da takardun a kotu, tare da kira ga ’yan Najeriya su haɗa kai wajen kare ikon ƙasar da martabarta.
Atiku ya kalubalanci FBI kan boye bayanan Tinubu
A wani labarin, an ji cewa Atiku Abubakar ya ce bai kamata FBI ta yi amfani da “barazana ga rayuka” a matsayin dalilin boye bayanan da doka ta ba da damar bayyana wa jama’a ba.
Ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da ya shafi abinci, magunguna da sauran bukatun yau da kullum saboda haka kawai bukatar a yi masu bayani.
Atiku ya ce kare jami’an FBI da majiyoyinsu ba yana nufin kare gaskiya daga ‘yan Najeriya ba.
Asali: Legit.ng


