Rasuwar Babban Jigon APC a Kano Ta Taɓa Shugaba Tinubu ana Shirin Fara Kamfen 2027
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi jimami da alhinin rasuwar babban jigon APC a jihar Kano, Alhaji Hamza Usman Darma
- Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Hamza Darma a matsayin amintaccen aboki kuma ɗan jam’iyya mai kishin ci gaba
- Shugaban ƙasa ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalansa haƙurin jure rashin kuma Ya shigar da shi Aljannar Firdausi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen ɗan siyasar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Alhaji Hamza Usman Darma.
Darma, wanda ya rasu a Kano ranar Juma’a da ta gabata bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da shekaru 76.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an gudanar da sallar jana’izarsa ranar Asabar a gidansa da ke Hororo, kusa da Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN), Kano, kafin a binne shi.
Tinubu ya yi alhinin rasuwar jigon APC
Shugaba Bola Tinubu, wanda ya bayyana cewa rasuwar ta taɓa shi, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da gwamnatin Kano bisa wannan rashi.
Hakan dai na kunshe ne cikin saƙon ta’aziyyar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar.
A sanaewar, Tinubu ya bayyana Darma a matsayin amintaccen aboki kuma mutum mai gaskiya, sannan ɗan jam’iyya APC mai kishin aiki wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tafiyar siyasar ci gaba.
APC ta gamu da babban gibi
Shugaban ya ce za a ji babban gibi sakamakon rasuwar marigayin, yana mai tuna irin gudummawar da ya bayar ga APC da kuma dangantakarsa ta ƙashin kai da shi.
Tinubu ya ce ya daɗe yana da kyakkyawar alaƙa da marigayin, yana mai cewa Darma ya yi fice wajen gaskiya, amana da jajircewa wajen ci gaban Jihar Kano da siyasar ci gaba a ƙasar.

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027
“Na san Darma a matsayin mutum mai gaskiya da amana tun lokacin da hanyoyinmu suka haɗu.
“Ya bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban Jihar Kano, kamar yadda ya yi wa tafiyarmu ta siyasar ci gaba da kuma APC,” in ji Tinubu.
Tinubu ya yaba da rikon addinin Darma
Shugaban Ƙasar ya kuma yaba da yadda Darma ya kasance mai kishin addinin Musulunci, yana mai tuna yadda marigayin ya kasance mai tsayawa kan ibadunsa.
“Abu mafi muhimmanci shi ne, Darma Musulmi ne mai tsoron Allah. Babu abin da ya isa ya hana shi zuwa masallaci a duk lokacin da ya ji kiran sallah,” in ji shi.
Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokan siyasarsa da iyalan APC a Jihar Kano, tare da jajanta wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa wannan babban rashi.

Source: Facebook
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya bai wa iyalan marigayin ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan rashi, tare da gafarta masa zunubansa da shigar da shi Aljannar Firdausi, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Barau ya yi alhinin rasuwar Darma
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar sanannen dan siyasa a jihar Kano, Alhaji Hamza Darma.
Barau ya mika sakon ta'aziyya ga iyalansa, yana mai bayyana cewa rasuwar Alhaji Hamza Darma babban rashi ne ga Kano da ma Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng

