FG: An kori ma'aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda

FG: An kori ma'aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda

- NEMA, hukumar bayar da agaji ta tarayya, ta sallami sabbbin ma'aikatan da ta dauka a shekarar 2018

- Hukumar NEMA ta ce ta sallami ma'aikatan ne saboda tun farko an daukesu ba tare da bin ka'idojin da suka kamata ba

- Sai dai, sabbin m'aikatan sun ce tun farko ma'aikatan NEMA sun nuna musu kyashi da kyama bayan an daukesu aiki

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta kori sabbin ma'aikatan da ta dauka su fiye da arba'in da biyu bayan sun shafe shekara guda babu albashi.

Daily Nigerian ta rawaito cewa na dauki sabbin ma'aikatan ne a watan Disambar shekarar 2019, watanni kalilan kafin a cire tsohon shugaban NEMA, Mustapha Maihaja.

Sabbin ma'aikatan sun samu rubutaccen sakon sanar da su janye aikin da aka daukesu a yayin da suke jiran sakon wuraren da za'a tura domin fara aiki a karkashin sabon shugaban NEMA, AVM Muhammadu Mohammed.

A cikin sakon da ta aike musu, NEMA ta sanar da sabbin ma'aikatan cewa an daukesu aiki ne ba bisa ka'ida ba, saboda ba'a bi ka'idojin da ya kamata ba kafin daukan sabbin ma'aikata.

An fara aikawa sabbin ma'aikatan sako a cikin watan Yuni na shekarar 2020, inda aka sanar da su cewa su dan dakata har zuwa lokacin da za'a kammala bincike akan daukansu aiki.

KARANTA: FG zata maye gurbin matsayin BVN da NIN bayan CBN ya gamsu da hujjar Pantami

A sako na biyu da aka aika musu a ranar 25 ga watan Janairu, 2021, NEMA ta sanar da sabbin ma'aikatan cewa sakamakon bincike ya nuna cewa ba'a daukesu aiki bisa ka'ida ba.

FG: An kori ma'aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda
FG: An kori ma'aikata fiye da 42 a NEMA bayan hanasu albashin shekara guda
Asali: Twitter

Takardar sakon, mai dauke da sa hannun Musa Zakari, mataimaki darekta a NEMA, ta sanar da sabbin ma'aikatan cewa an soke batun daukansu aiki.

KARANTA: Fahimta Fuska: Ganduje ya shirya muhawara tsakanin Abduljabar da manyan Malaman Kano

Sai dai, sabbin ma'aikatan, wadanda suka ajiye wasu ayyukansu domin komawa NEMA, sun kafe akan cewa sun bi duk wasu matakai da ya kamata kafin a kai ga daukansu aiki.

Ma'aikatan da ka sallama sun bayyana cewa hukumar NEMA ba ta taba basu ko sisi ba a matsayin albashi tun bayan daukansu aiki da kammala bude musu fayil a matsayin sabbin ma'aikata.

Sabbin ma'aikatan sun dora alhakin sallamarsu akan tsofin ma'aikatan NEMA wadanda tun farko suka nuna musu kuru-kuru cewa basa kaunar ganinsu a hukumar.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sanar da bullo da sabon shirin bayar da ilimi mai taken ASP (Alternate School Programme).

ASP sabon shirin gwamnatin Buhari ne da zai tabbatar da bayar da ilimi kyauta ga yara marasa galihu da basa zuwa makaranta.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa burin gwamnatinsa shine bayar da ilimi ga dukkan yaran da ke Nigeria.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel