Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Tsawa ta halaka mutane 7 a garin Yola

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Tsawa ta halaka mutane 7 a garin Yola

Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai sanadiyar tsawa a ranar Alhamis a Yola.

Mista Abani Garki, shugaban kula da ayyukan hukumar a jihohin Adamawa da Taraba, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Yola a ranar Asabar.

Ya jero wadu daga cikin yankunan da abun ya shafa a matsayin Runde-Baru, Wuro-Jabbe, Damilu, Yolde-Pate, Bachure, Kofare da kuma Jambutu da sauransu, duk a kananan hukumomin Yola ta kudu da Yola ya arewa.

Garki ya daura alhakin yawan ambaliyar ruwa da ake samu a yankunan kan sakacin mutanen garuruwan, cewa mazauna yankin suna kewaye filayensu da siyar dasu ba tare da bin tsari yadda ya kamata ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama Omoyele Sowore

Ya shawarci gwamnatin Adamawa da ta duba lamuran filaye sannan ta bukaci mutane da su guji gini a yankunan ambaliyar ruwa.

A wani labarin kuma, mun ji cewa ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da Tony Okecheme, direktan sashin kudi a Babban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma'a 2 ga watan Augusta inda ake juyayin gano shi da ransa.

Vanguard ta ruwaito cewa direktan da direbansa suna hanyarsu ta zuwa filin tashi da saukan jirage na Nnamdi Azikwe ne lokacin da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a shataletalen Galadinma da ke Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng