Kazamin Fada Ya Barke Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, an Kashe 'Yan Ta'adda da Dama

Kazamin Fada Ya Barke Tsakanin Mayakan ISWAP da Boko Haram, an Kashe 'Yan Ta'adda da Dama

  • An samu kazamin fada tsakanin JAS da ISWAP a wasu yankunan Dajin Sambisa, Borno, inda aka samu asarar rayuka.
  • Rikicin ya shafi sama da mambobin JAS 30, ciki har da mata da yara da ke yankunan da abin ya shafa.
  • Hakazalika, wani kwamandan JAS, mayaka uku da wata mata sun mika wuya ga dakarun rundunar sojojin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - An samu kazamin rikici tsakanin bangarorin kungiyar Boko Haram da ISWAP masu adawa da juna a wasu sassan Dajin Sambisa da ke Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Rahotanni sun ce an samu asarar rayuka da dama a tsakanin mayakan bangaren JAS yayin arangamar, wadda ta faru a wasu sansanoninsu da ke cikin dajin.

Mayakan Boko Haram da ISWAP sun gwabza fada
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Masani kan harkojin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da zaman sulhu na siyasa, shugaban APC ya faɗi ƙasa matacce

Rikici ya barke a sansanonin ‘yan ta’adda

Bayanan sirri sun nuna cewa fadan ya barke a yankunan Zarmari, Bula Daloye da Chirchor da ke cikin Dajin Sambisa.

Rahotannin sun ce arangamar ta shafi sama da mambobin JAS 30, ciki har da mata da yara da ke yankunan da rikicin ya rutsa da su.

Wasu majiyoyi da suka san abin da ya faru sun ce an samu gagarumar asara a bangaren JAS, yayin da wasu daga cikin wadanda suka tsira suka tsere zuwa cikin dazuzzukan da ke kusa.

Sojoji sun kara sanya ido

Sabon rikicin ya sake bayyana irin kishin da ke tsakanin bangarorin JAS da ISWAP wajen neman iko da yankuna da albarkatun da ke yankunan Borno.

Bayan arangamar, jami’an tsaro da ke aiki a Bama da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da yankin sun kara sanya ido tare da bibiyar motsin mayakan a wuraren da rikicin ya faru.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi barin wuta kan yan ta'adda, miyagu da dama sun rasa rayukansu

Kwamandan JAS da wasu sun mika wuya

A wani sabon ci gaba, wani kwamandan JAS, mayaka uku da wata mata sun mika wuya ga dakarun Rundunar Sojin Najeriya ta 21 Special Armoured Brigade da ke gudanar da ayyuka karkashin Operation Hadin Kai da Operation Desert Sanity V.

Rahotanni sun ce mutanen biyar sun mika wuya da misalin karfe 11:00 na dare ranar Juma’a, 21 ga Agusta, a yankin Kumburi na Karamar Hukumar Bama.

An bayyana kwamandan da sunansa Ishiaku Agah, yayin da mayakan ukun suka hada da Sulieman Yaga, Iburija Chari da Ba’ana Modu. Matar da ta mika wuya tare da su an bayyana sunanta da Falmata Modu.

Mutanen sun fito ne daga yankin Bula Daloye kafin su mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya.

Rikicin da ya barke tsakanin JAS da ISWAP na ci gaba da nuna rarrabuwar kawuna da gwagwarmayar neman iko tsakanin bangarorin biyu a wasu sassan Jihar Borno.

Mayakan ISWAP sun mika wuya
Wasu mayakan ISWAP da suka mika wuya ga sojoji Hoto: @zagazolamakama
Source: Twitter

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa fargaba ta bazu tsakanin shugabannin kungiyar 'yan ta'addan Islamic State West Africa Province (ISWAP), bayan kashe babban kwamandanta.

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta samu nasarar kawar da wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna WAL-GEGE a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng