Badakala: Jam’iyyar PDP ta jefi Yemi Osinbajo da laifin wawurar kudi a NEMA

Badakala: Jam’iyyar PDP ta jefi Yemi Osinbajo da laifin wawurar kudi a NEMA

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta bukaci mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya wanke kansa daga zargin hannu a wata badakala da aka tafka a hukumar NEMA.

PDP ta bukaci Farfesa Yemi Osinbajo ya fito ya kare kansa daga zarginsa da ake yi da ta cewa a wawurar wasu Naira biliyan 5.8 daga asusun hukumar da ke bada agajin gaggawa.

A wani jawabi da aka fitar a ranar litinin, 4 ga watan Mayu, PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama tsohon shugaban hukumar ta NEMA da ya sauke.

Kola Ologbodinyan shi ne ya fitar da jawabi a madadin jam’iyyar adawar dazu nan a Abuja. PDP ta ce kokarin rufa-rufa ta sa gwamnatin Buhari ta tsige Alhaji Mustapha Maihaja.

PDP ce: “Jam’iyyarmu ta na ganin cewa kin binciken tsohon shugaban NEMA yunkuri ne na kare wasu manya a cikin gwamnatin APC da su ke da hannu a badakalar da aka tafka.

KU KARANTA: Dalilin jami'an tsaro na rufe fadar Sarkin Daura inji Gwamna Masari

“A daidai wannan lokaci an bar talakawan da aka warewa kudin nan su na fama da wahala. Ka da sauke Maihaja ya sa a rufe binciken ofishin mataimakin shugaban kasa Osinbajo.”

“Jam’iyyar nan ta tuna cewa mataimakin shugaban kasa bai iya kare kansa daga rahoton da majalisar wakilai ta fitar na cewa an sace Naira biliyan 33 daga asusun NEMA ba.”

Jami’in jam’iyyar ta PDP ya kara da cewa: “Bayan wasu Naira biliyan 5.8 da aka zara daga baitul malin kasa a lokacin da Osinbajo ya ke kan kujerar shugaban rikon kwarya.” Inji sa.

Ologbodinyan ya yi kira ga EFCC ta yi gaggawar damke Maihaja domin yi masa tambayoyi, a kuma daure shi idan an same shi da laifin taba dukiyar jama’a a lokacin da ya ke ofis.

Osinbajo ne shugaban majalisar da ke kula da hukumar NEMA. Sai dai shugaban wata kungiya ta magoya bayan shugaba Buhari, Niyi Akinsuyi ya yi watsi da wannan zargi na PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel