Bayan Kalaman Wike, NDC Ta Fadi Yadda Ta Shirya Kwace Abuja a 2027
- Reshen Kudu maso Gabas na NDC a Abuja ya ce yana shirin tara kuri’u miliyan daya domin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027
- Jam’iyyar ta ce za ta hada al’ummar kabilar Igbo da ke Abuja da sauran sassan FCT karkashin inuwar NDC domin karfafa yakin neman zabe
- NDC ta yi wannan batu ne bayan kalaman Nyesom Wike, Ministan Abuja da ke tallata tazarcen Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Reshen Kudu maso Gabas na jam’iyyar NDC a Babban Birnin Tarayya Abuja, ya ce yana da burin samun kuri’u akalla miliyan daya ga dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a zaben 2027.
Shugaban reshen Kudu maso Gabas na NDC a Abuja, Mike Nwosu, ne ya bayyana hakan ranar Asabar 22 ga watan Agusta, 2027.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Tun kafin lokaci, an kammala tsara wanda zai lashe zaben shugaban ƙasa a 2027

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa ya fadi haka ne a yayin da ya jagoranci mambobin jam’iyyar daga kananan hukumomin Abuja shida zuwa ziyarar nuna goyon baya ga mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da Kudu maso Gabas, Teddy Obey.
Shirin NDC game da Abuja a 2027
Tribune Online ta kawo labarin cewa Nwosu ya ce manufar ziyarar ita ce nuna godiya ga shugabannin jam’iyyar na kasa bisa bai wa yankin Kudu maso Gabas damar samar da dan takarar shugaban kasa.
Ya ce yanzu nauyin da ke kan yankin shi ne ya mayar da wannan karamci ta hanyar tattara magoya baya tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar da ‘yan takararta a zaben 2027.

Source: Facebook
Nwosu ya ce za su fara wani gagarumin gangamin wayar da kan jama’a kafin fara yakin neman zabe, inda za su mayar da hankali wajen ganin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar ya samu gagarumin goyon baya a FCT.

Kara karanta wannan
Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027
Ya ce:
“Za mu hada mutane da ba su yi kasa da miliyan daya ba a Abuja. Muna son hada dukkan ‘yan kabilar Igbo da ke Abuja da FCT wuri guda karkashin inuwa daya, wato NDC.”
Nwosu ya jinjina takarar Obi
Nwosu ya bayyana fitowar Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a matsayin wani babban mataki na kara bai wa Kudu maso Gabas damar shiga harkokin shugabancin kasa.
Ya ce yankin ya dade yana neman karin damar shiga harkokin siyasar kasa, don haka goyon bayan da NDC ta bai wa dan takara daga yankin wata dama ce da ya kamata a yi amfani da ita yadda ya kamata.
Shi ma babban mai ba shugaban NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, shawara kan harkokin fasaha, VinMartin Ilo, ya ce ziyarar ta nuna godiyar Kudu maso Gabas ga damar da jam’iyyar ta bai wa yankin.
Abin da Wike ya ce kan zaben 2027

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027
A wani labarin, kun ji cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce sauye-sauyen siyasa a ƙasar nan sun ƙara ƙarfafa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.
Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa duba da abubuwan da ke faruwa, an riga an kammala babban zaben shugaban kasa na 2027 kuma har an san wanda ya yi nasara.
Ministan Abuja Wike ya yi watsi da batun akwai babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, yana mai cewa alami sun nuna Tinubu ne zai ci zabe idan an jefa kuri'a a 2027.
Asali: Legit.ng