Guguwar iska ta rusa gidaje 1,000 a Kebbi da Zamfara

Guguwar iska ta rusa gidaje 1,000 a Kebbi da Zamfara

- Rahotanni sun kawo cewa tun da aka shiga kakar ruwan saman bana, guguwar iska ta rusa gidaje 1000 a jihar Kebbi da Zamfara

- Shugaban ofishin gudunar da ayyukar hukumar na jihar Sokoto, Mista Suleima Muhammad, ya tabbatar da hakan ne wa manema labarai a jihar Sokoto

Rahotanni sun kawo cewa tun da aka shiga kakar ruwan saman bana, guguwar iska ta rusa gidaje 1000 a jihar Kebbi da Zamfara, inji hukumar bada agajin gaggawa wato NEMA.

Shugaban ofishin gudunar da ayyukar hukumar na jihar Sokoto, Mista Suleima Muhammad, ya tabbatar da hakan ne wa manema labarai a jihar Sokoto inda ya cewa mutane da dama sun ji rauni game da lamarin amma babu wanda ya rasa ransa.

Da yake bayanin iya adadin gidajen da guguwar ta rusa, ya ce gidaje 800 suka rushe a karamar hukumar Maiyama da ke jihar Kebbi a ranar 30 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Shekarau ya janye barazanar maka rundunar ‘yan sanda a Kotu

A cewar Muhammad, akalla gidaje 200 suka rushe a kananan hukumomin Anka, Maradun da Birnin dake jihar Zamfara a ranar 2 ga watan Mayu.

“Abun murna shine ba a rasa rayukan kowa ba a lokacin afkuwa hadarin sai dai kawai wasu da suka samu jin rauni" inji shi.

Mohammad ya ce hukumar tuni ta tallafawa wadanda abun ya shafa da kayayyakin amfanin yau da kullun wanda suka hada da bargo, kayayyakin abinci, cementi, pallen-kwanu da makamincin su.

Ya ce, ya lura da cewa an samu irin wannan hadarin a kananan hukumomin Tambuwal da Shagari da ke jihar Sokoto a ranar 14 ga watan Mayu amma ya kasa bada iya adadin gidajen da suka rushe.

"A yanzu haka jami’an hukumar na nan suna gudunar da bincike akan barnar da iskar yayi, domin bada kayayyakin agaji ga wadanda abun ya shafa," a cewar Muhammad.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nakasassu sun koka ma minista akan halin da suke ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: