Masu Garkuwa Da Mutane
An yi gumurzu yayin da 'yan bindiga suka sace wata yarinya mai shekaru bakwai a kauyen Yangoji da ke Kwali a babban birnin Tarayya Abuja a safiyar jiya Laraba.
Ƴan bindiga sun buƙaci da a biya su N9m a matsayin kuɗin fansar basaraken da suka sace a Abuja da wasu mutum biyu. Ƴan bindigan sun ce kowane a biya masa N3m.
Jami'an 'yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da kubutar da yara tara da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Asabar a karamar hukumar Maradun ta jihar.
Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu sace mutane ne sun yi garkuwa da shahararen mai wa'azin nan na gidan talbijin, Rabaran Mike Ochigbo a jihar Adamawa.
'Yan sanda a jihar Nasarawa sun yi nasarar kama masu garkuwa da mutane su 26 tare da kubutar da mutane biyu da masu garkuwar suka sace. Jami'in hulda da jama'a.
Gwamnatin tarayya ta ce ta ware N15bn a kasafin kudin shekarar 2023 don ba da tsaro ga dalibai da ke makaranta daga hare-hare da kuma masu garkuwa da mutane.
Ƴan bindiga sun sake kai mummunan hari a birnin tarayya Abuja, sun yi awon gaba da mutum 15. Ƴan bindigan sun kai harin ne dai a Pegi cikin ƙaramar hukumar Kuje
Rundunar ƴan sandan jihar Delta, ta cafke wani ƙaramin yaro da abokansa biyu, bisa zargin shirya yadda za a yi garkuwa da shi, da neman N20m a wajen iyayensa.
An kama wata mata da ta yi garkuwa da 'yarta a Kano bayan ta dauketa ta kai ta gidan 'yan uwanta a Madobi don a ajiye yarinyar da nufin cewa zata yi tafiya.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari