Matashi Mai Shekaru 23 Ya Hallaka Farfesa da Kaninsa cikin wani Irin Yanayi

Matashi Mai Shekaru 23 Ya Hallaka Farfesa da Kaninsa cikin wani Irin Yanayi

  • Rundunar 'yan sandan Benue ta kama wani dan Arewa da ake zargin ya hallaka Farfesa da kannensa
  • An kama matashin mai shekaru 23 bisa zargin hannu a kisan Farfesa Gabriel Nyityo a Makurdi da ke Benue
  • Kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya ce jami'ai sun samu kiran gaggawa zuwa yankin Adaka inda suka tarar da gawarwakin Farfesa Nyityo da ƙanensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Rundunar 'yan sandan Benue ta sanar da cafke wani matashi da ake zargin ya hallaka Farfesa da kannensa.

Matashin mai suna Abdullahi Usman, mai shekaru 23 ya shiga hannun jami'an sanda a birnin Makurdi da ke jihar Benue kan tuhumar da ake yi masa.

Matashi ya kashe Farfesa a Benue
Sufeta-janar na ƴan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Mai magana da yawun rundunar, DSP Udeme Edet, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar, sannan aka rabawa manema labarai a Makurdi, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Zargin da ake yi wa matashi a Benue

Rahotanni sun ce ana zarginsa da hannu a kisan malamin Jami'ar Benue, Farfesa Gabriel Nyityo lamarin da ya tayar da hankalin mutanen yankin.

A cewarsa, jami'an 'yan sanda na sashen 'D' sun samu kiran gaggawa daga yankin Adaka, inda suka isa suka tarar da gawarwakin mutane biyu.

Sanarwar ta ce Farfesa Gabriel Saawua Nyityo mai shekaru 58 da ƙanensa, Iorngee John Nyityo mai shekaru 19, wasu mahara da ba a tantance ba suka kashe.

Rundunar ta ce an kama Abdullahi Usman, ɗan asalin garin Awe a Nasarawa, dangane da wannan laifi, kuma bincike na ci gaba domin kamo sauran waɗanda ake zargi.

An kama matashi kan zargin kisan Farfesa
Taswirar jihar Benue da ke fama da hare-haren ƴan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka kashe Farfesa da kaninsa a Benue

Rahotanni sun nuna cewa an kashe Farfesa Nyityo da ƙanensa ne a gidansu da ke yankin Adaka, ƙaramar hukumar Makurdi, da sanyin safiyar ranar Laraba 8 ga watan Yulin shekarar 2026.

Ko da yake malaman jami'ar suna yajin aiki a halin yanzu, kisan Farfesa Nyityo na sashen Tarihi ya girgiza mazauna yankin Adaka da al'ummar Jami'ar Benue.

Kara karanta wannan

An harbe 'yan bindiga har lahira bayan gwabza fada da 'yan sanda

'Yan sanda sun tabbatar da cewa za su ci gaba da bincike mai zurfi domin gano duk masu hannu a wannan kisan tare da gurfanar da su gaban shari'a, cewar Daily Post.

Jihar Benue na daga cikin jihohi a Arewa ta Tsakiya da ke fama da rikice-rikice ciki har da garkuwa da mutane wanda ya yi sanadin rasa rayukan mutane da dukiyoyinsu.

Har ila yau, rikicin manoma da makiyaya ya sake rura wutar kabilanci duba da cewa mafi yawa makiyaya Fulani sannan manoma kuma yana asalin jihar ne.

Yan bindiga sun sace Fasto a Benue

Mun ba ku labarin cewa 'yan bindiga sun sake yin aika-aika a jihar Benue bayan da suka yi garkuwa da wani fasto da ke jagorantar wani coci.

Hatsabiban 'yan bindigan sun sace faston ne tare da wasu mambobin cocinsa bayan sun kai harin da ya sake jefa mutane cikin firgici.

An mika kokon bara ga jama'a da su yi addu'o'i domin ganin mutanen da aka sace sun kubuta daga hannun 'yan bindiga cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.