Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Babban Birnin Jiha, Sun Sace Mutum 8 a Gida Daya

Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Babban Birnin Jiha, Sun Sace Mutum 8 a Gida Daya

  • Wasu miyagun masu garkuwa da mutane sun kutsa har cikin gidan basarake inda suka sace matansa biyu da ‘ya’ya shida
  • Lamarin ya faru ne a gidan basaraken da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba amma ‘yan sanda sun ce suna kokarin ceto su
  • Jastis Sani Muhammad mai ritaya, shi ne babban basaraken Mutumbiyu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba

Jalingo, Taraba - Garkuwa da Mutane ya sake dawowa jihar Taraba. Wasu miyagun ‘yan bindiga a jihar sun sace mutum takwas ‘yan gida daya duk daga gidan wani barasake na jihar.

‘Yan bindiga
Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Babban Birnin Jiha, Sun Sace Mutum 8 a Gida Daya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa, an sace mata biyu da ‘ya’ya hudu na sarkin Mutumbiyu da ke Karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba, Jastis Sani Muhammad mai ritaya.

Mummunan lamarin ya faru ne a gidan basaraken da ke Jalingo, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun sace daliban makarantar firamaren gwamnati a wata jihar Arewa

Rundunar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi yace ana ta kokarin ceto wadanda aka sace.

Yan bindiga sun farmaki coci, sun sace masu bauta 25

A wani labari na daban, miyagun ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Jan Tsauni da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Sun bar babban faston cocin a jigace inda suka sace wasu masu bauta 25 a cocin bayan ruwan wutan da suka yi.

Yan Sanda sun cafke ‘dan fim din da ya sokawa makwabcinsa wuka a kirji

A wani labari na daban, wani jarumin fim din kudancin Najeriya ya sharbawa makwabcinsa wuka a kirji kan kudin Nepa.

An kawo takardar wuta kuma aka bukacesu da su biya N1,000 don harhada kudin amma makwabcin yace ba zai bayar ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya

Wannan lamarin ya fusata jarumin inda ya hanzarta shiga daki tare da dauko wuka ya sharia masa a kirji.

Tuni sauran wadanda ke wurin suka kwashi makwabcin zuwa asibiti yayin da ‘yan sanda suka cafke mai laifin.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace an kai shi asibiti saboda raunikan da ya samu shi ma.

Ya amsa cewa ya aikata laifin kuma a halin yanzu yana hannun hukuma inda ake cigaba da bincike kafin kai shi kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel