Amurka Ta kai Hare Hare Iran ana Jana'izar Ali Khamenei

Amurka Ta kai Hare Hare Iran ana Jana'izar Ali Khamenei

  • Sojin Amurka sun kai hari kan wurare sama da 80 a Iran ciki har da jiragen ruwa kanana 60 na IRGC da ke mashigar Hormuz
  • Iran ta rama ta harba makami da jiragen sama marasa matuka zuwa sansanonin sojin Amurka 85 da ke Bahrain da Kuwait
  • Kasashen Qatar da Saudiyya sun zargi Iran da kai hari kan jiragen ruwan man fetur din su yayin da suke ratsa Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Amurka ta kai hari mai karfi kan Iran bayan da wasu jiragen ruwa uku na kasuwanci suka fuskanci hare-hare a mashigar Hormuz a ranar Talata.

Bayan labarin ya bazu, hukumar watsa labarai ta jihar Iran ta bayyana cewa an kai hari kan tsibirin Qeshm da birnin Bandar Abbas da kauyen Sirik, inda wasu mutane suka jikkata.

Kara karanta wannan

An saki bama bamai yayin da shugaban Faransa ya isa kasar Syria

Ayatollah Ali Khamenei da Donald Trump
Jirgin yaki a tsakiyar Ayatollah Ali Khamenei da Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta kai hari Iran

A sakon da suka fitar a Facebook, sojin Amurka sun bayyana dalilin hare-haren na cewa sun yi shi ne domin a kakaba wa masu kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci takunkumi.

Rundunar sojin Amurka ta farmaki Iran ne a daidai lokacin da jama'ar kasar ke jana'izar Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Iran ta farmaki Amurka

Da safiyar ranar Laraba, IRGC ta sanar da cewa ta rama ta kai hari kan wurare 85 masu muhimmanci na sojin Amurka a Bahrain da Kuwait.

A cikin sanarwar, IRGC ta ce an yi amfani da makami da kuma jiragen sama marasa matuka, kuma an lakume hedkwatar rundunar sojan ruwan Amurka da sansanin jiragen sama da ke Kuwait.

Kafin harin Amurka, mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya sanya wa abin suna keta yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca kaca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Haka ma, Amurka ta janye wata shaida ta wucin gadi wadda ta dage takunkumin man fetur kan Iran, abin da Iran ta yi Allah wadai da shi ta ce ya nuna rashin amincin gwamnatin Amurka.

BBC ta rahoto cewa ma'aikatar harkokin wajen Iran ta yi barazana cewa Tehran za ta dauki duk matakan da ta ga ya dace don kare muradunta da tsaron kasa.

Qatar da Saudi sun zargi Iran

Gwamnatocin Qatar da Saudiyya ma sun fito sun yi tir da hare-haren, kowanne daga cikinsu yana mai cewa an farmaki jirginsa na ruwa yayin da yake ratsa mashigar ko kusa da shi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al Ansari, ya ce kasar tasa ta daurawa Iran cikakken alhakin wani harin kai tsaye da ake zargin an kai kan jirgin Al-Rekayyat.

A daya bangaren, kasar Saudiyya ma ta sanar da cewa Iran ta kai hari kan jirinta na Wadyan yayin da yake ketare mashigar Hormuz.

Hanyar Hormuz a Iran
Wasu jirage sun nufi mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daga bangaren Iran, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen, Esmail Baghaei, ya yi watsi da zargin da kasashen suka yi.

An lassasa Amurka a kwallo

Kara karanta wannan

An saki bidiyon bama baman da Putin ya harba babban birnin Ukraine

A wani labarin, mun kawo muku cewa an yi wa 'yan kwallon Amurka cin kaca a gasar cin kofin duniya da aka buga duk da kokarin Donald Trump.

Kwana daya kafin wasan, shugaba Trump ya kira hukumar FIFA a waya domin ta janye jan katin da ta ba fitaccen dan kwallon Amurka.

Duk da FIFA ta janye jan katin, lamarin da ya ba dan wasan damar taka leda da Belgium, Amurka ba ta kai labari ba, an ba ta kashi da ci 4 -1

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng