‘Yan bindiga Sun Shiga Gida, Sun yi Nasarar Awon Gaba da Hakimi a Arewacin Najeriya

‘Yan bindiga Sun Shiga Gida, Sun yi Nasarar Awon Gaba da Hakimi a Arewacin Najeriya

  • Hakimin Chawai a garin Kauru ta jihar Kaduna, Cif Joshua Ahmadu yana hannun ‘yan bindiga
  • Mutanen garin sun sanar da hukuma, sannan an fadakar da jami’an tsaro domin a dauki mataki
  • Jami’an tsaro sun bayyana cewa su na bakin kokarinsu wajen ganin an ceto Mai martaba Ahmadu

Kaduna - ‘Yan bindiga sun dauke Cif Joshua Ahmadu, wanda shi ne Hakimin Chawai a karamar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Shugaban kungiyar CDA ta mutanen Chawai, Abel Adamu ya tabbatar da aukuwar wannan labari.

A ranar Laraba, Abel Adamu ya shaidawa Duniya an yi awon gaba da Mai martaban.

Kamar yadda Abel Adamu ya bada sanarwa, mazauna yankin su na bakin kokarinsu na ganin yadda za a kubutar da Joshua Ahmadu.

Jawabin Shugaban CDA, Abel Adamu

Kara karanta wannan

Mummunan karshe: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 3, sun ceto mutum 16 a wata jihar Arewa

“Tuni an sanar da hukumomin da ya kamata da shugabannin jami’an tsaro da ke aiki na musamman a kasa domin su yi gaggawar ceto Basaraken

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mu na kira ‘ya ‘yan kasar Tsoma, su dage da addu’a wajen ganin an ceto hakiminsu, ya dawo.”

- Abel Adamu

‘Yan bindiga
Wani Jami'in tsaro a bakin aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Yan sanda sun tabbatar da lamarin

Jawabin da kakakin rundunar ‘yan sanda, Raphael Joshua ya fitar ya nuna cewa ‘yan bindiga sun je har gida ne suka dauke Basaraken.

Jami’an tsaro sun ce ‘yan bindiga sun je gidan Hakimin a yankin Zambina da kusan karfe 9:30 na daren Laraba, suka yi awon gaba da shi.

A jawabin da Joshua ya fitar a madadin rundunar ‘yan sanda, ya yi kira ga matasan Chawai su bada muhimmanci kan sha’anin tsaro.

PM News ta ce ‘yan sanda su na zargin matasan Chawai da kin taimakawa jami’an tsaro wajen ganin an tsare rayuka da dukiyarsu.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun ‘yan sanda na shiyyar Kafanchan sun ziyarci iyalin Hakimin, sun tabbatar masu za a kubuto da shi.

Matsalar tsaro a Katsina

Jam'iyyar LP ta shirya taron siyasa, sai aka fuskanci akwai matsalar tsaro, dole aka hakura. An ji labari hakan ya faru ne a Katsina.

Majiya ta ce an samu bayanai masu ban tsoro, a dalilin haka ne Peter Obi ya fasa ganawa da 'yan gudun hijira, mata da matasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel