Yan Sanda Sun Kama Matasa Uku Kan Sace Yarinya Yar Shekara 6 a Kano

Yan Sanda Sun Kama Matasa Uku Kan Sace Yarinya Yar Shekara 6 a Kano

  • Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta kama wasu matasa uku kan yin garkuwa da wata yarinya yar shekara 6
  • Kakakin yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce matasan sun sace yarinyar ne a farkon watan Janairu sannan suka nemi a biya naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa
  • Yan sandan sun bayyana cewa an ceto yarinyar mai suna Fatima Abubakar cikin koshin lafiya

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta cika hannu da wasu matasa uku kan zargin garkuwa da wata karamar yarinyar yar shekara 6.

Kamar yadda rundunar yan sandan ta sanar, matasan da aka kama sun hada da Abdulrazak Ibrahim, Aliyu Salisu, da Mohammed Ibrahim wadanda dukkaninsu yan shekaru 19 ne, rahoton TheCable.

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Kama Matasa Uku Kan Sace Yarinya Yar Shekara 6 a Kano Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda aka kama masu laifin, yan sanda

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, Gambo Isah, kakakin yan sandan jihar Katsina, ya ce wadanda ake zargin sun hada kai sannan suka sace yarinyar a Kwatas din Bachirawa da ke jahar Kano a ranar 6 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Atiku da Peter Obi Sun Shiga Matsala, Sun Yi Gagarumin Rashi Ana Gab Da Zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isah ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun bukaci iyayen yarinyar su biya naira miliyan 2 a matsayin kudin fansar ta.

Kakakin yan sandan ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne a wajen karbar naira miliyan biyun na kudin fansa.

Isah ya ce:

"Sun sace wata Fatima Abubakar, yarinya mai shekara 6 a Kwatas din Bachirawa, jihar Kano a ranar 06/01/2023 da misalin karfe 1100hrs sannan suka yi awon gaba da ita zuwa jihar Katsina sannan suka bukaci a biya naira miliyan biyu kudin fansa.
"An kama wanda ake zargin (Aliyu Salisu wanda aka fi sani da Chilo) hannu dumu-dumu a wajen karbar kudin fansar.
"A yayin bincike, an sace sauran miyagun sannan aka ceto yarinyar cikin koshin lafiya."

Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu da zaran an kammala bincike, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Ribas: ‘Yan Sanda Sun Damke Yaro Mai Shekaru 17 da Yayi wa Mata 10 Ciki

Fasto ya shiga hannu kan zargin garkuwa da kansa don karbar kudin fansa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani limamin coci a jihar Filato ya shiga hannun yan sanda sakamakon zarginsa da ake yi da garkuwa da kansa don amsar kudin fansa daga mabiyansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel