Miyagun da Suka Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Fadi Abin da Suke Bukata

Miyagun da Suka Yi Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Fadi Abin da Suke Bukata

  • ‘Yan ta’addan da ake zargin sun sace wasu fasinjojin jirgin kasa a jihar Edo sun tuntubi ‘yanuwansu
  • Miyagun ‘yan bindigan su na neman a biya kudin fansar N20m a kan duk mutumin da ke hannunsu
  • Hakan na zuwa ne a lokacin da jami’an tsaro da hukumomi suka yi alkawarin ceto wadanda aka dauke

Edo - Masu garkuwa da mutanen da suka dauke Bayin Allah a tashar jirgin kas ana Ekehen a garin Igueben da ke jihar Edo, sun nemi a biya kudin fansa.

Rahoton da Daily Trust ta tattaro a ranar Litinin, ya nuna ‘yan bindigan sun tuntubi ‘yanuwan wadanda suka dauke, su na bukatar kowa ya biya N20m.

Wani jagoran matasa a yankin da abin ya faru, Benson Ordia ya tabbatar da lamarin, ya kuma bayyana cewa gwamnati tayi alkawarin kubutar da mutanen.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Shi kuwa SP Chidi Nwanbuzor wanda shi ne Mai magana da yawun ‘yan sanda na reshen jihar Edo, ya ce bai san da maganar neman kudin fansar ba.

Kowa zai fanshi kan shi da N20m

A rahoton da aka samu daga jaridar Vanguard, an tabbatar da cewa ‘yan ta’addan su na neman N20m daga hannun ‘yanuwan kowane mutum da aka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin garin ya ce ya samu labari ne a wajen jami’an tsaro. ‘Yan sanda sun yi alkawarin za suyi bincike domin su gano gaskiyar wannan magana.

Jirgin kasa
Jirgin kasan Warri-Itakpe Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

A matsayinsa na Darektan kungiyar Esan Youth for Good Governance & Social Justice ta matasa, Odia ya ce mutanen ba su da hanyar samun miliyoyin.

Ina za a gan su - Benson Ordia

“Zan iya fada maka masu garkuwa da mutanen sun bukaci N20m, gaba daya su na neman N620m. Ban san ta ya talakawa za su hada kudin nan ba.”

Kara karanta wannan

Ana Zanga-Zanga, ‘Yan APC Sun Tada Rigima kan Zargin Shugabanni da Satar $1.5m

- Benson Ordia

Odia ya fadawa Punch cewa ya kamata hukuma ta kara kokarin wajen ganin yadda za a ceto wadannan mutane da aka yi awon gaba da su a ranar Asabar.

Matashin ya shaida cewa Ministan sufuri na kasa, Mu’azu Sambo da shugaban NRC watau Fidel Okhiria, sun ziyarci Igueben bayan wannan abin da ya faru.

A cewarsa, hukumomin sun yi alkawarin za su yi amfani da jirage masu saukar ungulu domin a gano duk inda aka boye fasinjojin a cikin kungurmin jeji.

An dauke Alkali

A lokacin da aka tunanin za a ceto wadanda aka dauke, sai ga labari miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban kotun gargajiya ta Igueben a Edo.

An gano cewa, alkalin tana hanyarta ta zuwa wani zaman kotu ne yayin da miyagun suka sace ta. Har zuwa yanzu dai ba a samu labarin kubutar da ita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel