An Kama Fasto Albarka Kan Yin Garkuwa Da Kansa Har Sau 2 Yana Karbar Kudin Fansa Daga Mabiyansa A Plateau

An Kama Fasto Albarka Kan Yin Garkuwa Da Kansa Har Sau 2 Yana Karbar Kudin Fansa Daga Mabiyansa A Plateau

  • Yan sanda sun yi nasarar cafke wani fasto mai suna Albarka Sukuya kan shirya garkuwa da kansa don mabiya su tara masa kudin fansa
  • Fasto Sukuya ya yi garkuwa da kansa har sau biyu, da farko aka biya N400,000 sannan karo na biyun aka biya N200,000 a Jos, Plateau
  • Malamin addinin kiristan ya ce ambaci sunan mutane uku da suke shirya wannan yaudarar tare, an kama biyu cikinsu, ana neman na karshen

Jihar Plateau - Yan sanda sun kama wani fasto mazaunin jihar Plateau kan yin garkuwa da kansa tare da karbar kudin fansa daga hannun mambobinsa, rahoton The Nation.

Alfred Alabo, mai magana da yawun yan sandan Plateau, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce an kama wanda ake zargin ne a watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kera Motar Wasan Tsere Da Hannunsa, Ya Tuka Ta a Hanyar Edo, Bidiyon Ya Yadu

Taswirar Plateau
An Kama Fasto Albarka Kan Yin Garkuwa Da Kansa Har Sau 2 Yana Karbar Kudin Fansa Daga Mabiyansa A Plateau. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce ya sha shirye garkuwa da kansa domin ya yaudari mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Kalamansa:

"Yan sanda sun gano wani mummunan abin da wani Fasto Albarka Sukuya na Jenta Apata, Jos, ke aikatawa, wanda sau da yawa ya shirya garkuwa da kansa tare da abokan harkallarsa suna karbar kudin fansa daga mabiyansa.
"Kafin sace shi da aka yi ta yi a ranar 14 ga watan Nuwamba da 15 ga watan Nuwamban 2022, inda aka biya N400,000 da N200,000, matsayin fansa, an fara zarginsa.
"Ta sahihan bayanan sirri, DPO na caji ofis na Nasarawa, CSP Musa Hassan ya gayyaci malamin addinin kuma ya fara bincike.
"Yayin bincike an gano cewa wanda ake zargin yana hada baki da wasu yan tawagarsa su yi garkuwa da shi don yaudara su karbi kudin fansa."

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

Kwamishinan yan sandan ya cigaba da cewa wanda ake zargin kuma ya bayyana cewa a ranar 1 ga watan Janairu ya kona motocci da keken abokan aikinsa a harabar ECWA Bishara 3 da ke Jenta, kamar yadda ya shaidawa yan sanda, Daily Trust ta rahoto.

Alabo ya kuma ce wanda ake zargin ya ambaci sunayen wasu mutum uku a tawagarsa, an kama biyu, daya kuma ana nemansa.

An kama matashin da ya yi garkuwa da kansa ya karbi kudin fansa daga hannun mahaifinsa

Wani matashi mai suna Isreal Emmanuel ya shiga hannun yan sanda saboda laifin garkuwa a kansa tare da karbar kudin fansa daga wurin mahaifinsa.

The Nation ta rahoto cewa Emmanuel da wasu abokansa uku ne suka shirya wannan mummunan lamari kawai don samun kudi daga mahaifinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164