Ginin Majalisar Dokokin Jihar Gombe Ya Rufta kan Mutane Ana tsakiyar Aiki
- Mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin da wasu bakwai suka jikkata bayan sabon ginin Majalisar Dokokin jihar Gombe ya rufta kan mutane
- Rahotanni daga jihar sun nuna cewa wannan ibtila'i ya faru ne yayin da ake ci gaba da aikin gina sabon zauren majalisar dokokin
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin rushewar ginin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Ginin Majalisar dokokin jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najerirya ya rufta kan mutane a yau Jumu'a, 10 ga watan Yulin 2026.
Rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da mutuwar mutum guda yayin da wasu bakwai suka samu raunuka bayan ginin Majalisar Dokoki da ake ginawa birnin Glmbe ya rufta.

Source: Original
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa lamarin ya afku ne yayin da ma'aikata ke gudanar da aikin ginin yau Juma'a, inda wasu daga cikinsu suka makale a karkashin baraguzan ginin kafin jami'an ceto suka kai dauki.
Hukumar NEMA ta tabbatar da lamarin
Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), reshen jihar Gombe, Ummanah Ahmed, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Ya bayyana cewa an garzaya da mutum uku daga cikin wadanda suka samu raunuka dabn-daban zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe domin samun kulawa daga likitoci.
Ahmed ya kara da cewa jami'an ceto da suka kai dauki wurin da taimakon jama'a sun kai wasu mutum biyar zuwa Asibitin Kwararru na Jihar Gombe domin ci gaba da jinyarsu.
Hukumomi sun fara gudanarda bincike
Shugaban na NEMA ya ci gaba da cewa wasu daga cikin wadanda suka jikkata sun samu munanan raunuka daban daban sakamakon ruftawar ginin majalisar.
Yunkurin da aka yi domi jin ta bakin kamfanin da ke gudanar da aikin ginin bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Har yanzu ba a gano musabbabin rushewar ginin ba, yayin da hukumomin da abin ya shafa ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano abin da ya jawo ibtil'in, wanda ya yi sanadin rasa rai.
Gwamnatin jihar Gombe karkashin Gwmana Muhammad Inuwa Yahaya, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance jan ruftawar ginin Majalisar ba kawo yanzu.
Gini ya yi ajalin mutum 5 a Legas
A wani rahoton, kun ji cewa mutum biyar sun rasu sakamakon ruftawar wani gini da ke lamba 13, kan titin Wilson Mba, a unguwar Maryland da ke jihar Legas.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Olufemi Damilola ya ce jami'£[ LASEMA sun yi nasarar ceto mutane biyar waɗandadukkansu maza ne da ransu daga wurin da ginin ya ruguje, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawar da ta dace.
Asali: Legit.ng

