Yan Bindiga Sun Farmaki Jihar Edo, Sun Yi Awon Gaba Da Tsohon Dan Majalisa

Yan Bindiga Sun Farmaki Jihar Edo, Sun Yi Awon Gaba Da Tsohon Dan Majalisa

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da Festus Edughele, tsohon dan a majalisar dokokin jihar Edo a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu
  • An tattaro cewa tsohon dan majalisar na hanyar zuwa garin Benin, Babban birnin jihar daga Orhionmwon don hawa jirgin sama zuwa Abuja lokacin da aka sace shi
  • Tsohon mai magana da yawun majalisar dokokin jihar, Festus Ebea ya tabbatar da faruwar al’amarin

Jihar Edo - Al’ummar Jihar Edo sun shiga halin fargaba a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu, yayin da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon dan majalisar dokokin jiha, Festus Edughele.

Jaridar Punch ya rahoto cewa an yi garkuwa da Edugheli yayin da yake hanyar zuwa garin Benin daga Orhionmwon a ranar Litinin.

Yan bindiga
Yan Bindiga Sun Farmaki Jihar Edo, Sun Yi Awon Gaba Da Tsohon Dan Majalisa Hoto: Update Nigeria
Asali: UGC

An yi awon gaba da dan majalisar kwanaki uku bayan sace fasinjojin jirgin kasa da wasu da ake zaton makiyaya ne suka yi a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Wani Mai Hannu a Garkuwa Fasinjojin Jirgin Kasa a Najeriya, Ya Fara Bayani

An tattaro cewa mutanen su 32 suna jiran isowar jirgin kasa da zai kwashe su daga Igueben da ke karamar hukumar Igueben a Edo zuwa Warri da ke jihar Delta a ranar Asabar, 7 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Festus Ebea, tsohon kakakin Majalisar jihar, Edughele na hanyarsa ya zuwa babban birnin jihar don hawa jirgin da zai kai sa Abuja lokacin da yan bindigar suka sace shi sannan suka yi daji da shi.

Ebea ya ce iyalansa na sane da batun sace shi kuma rundunar yan sanda a yankin na daukar mataki don kubutar da shi cikin gaggawa, rahoton Nigerian Tribune.

Hukumar NRC Ta Dakatar da Jirgin Kasa Na Jihar Edo

A wani labarin, mun ji cewa hukumar NRC ta sanar da rufe tashar Jirgin kasa ta jihar Edo har sai baba ta gani.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hukumar NRC Ta Rufe Tashar Jirgin Kasa da Yan Bindiga Suka Kai Hari

Hukumar jiragen kasar ta ce wannan matakin ya zama dole biyo bayan tabarbarewar matsalar tsaro da harin da yan bindiga suka kai tashar.

Kamar yadda hukumar ta NRC ta sanar a manhajar whatsapp wanda yan jarida suka samu, tace an rufe tashar ne har sai baba ta gani.

A tuna cewa wasu 'yan bindiga sun faramki Fasinjojin dake jiran jirgin kasa daga tashar Igueben, karamar hukumar Igueben ranar Asabar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng