Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Halaka Rayuka 5, Sun Sace Mutum 1

Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Halaka Rayuka 5, Sun Sace Mutum 1

  • Miyagun ‘yan ta’adda sun kai hari kauyen Gambar Sabon Layi da ke Tafawa Balewa a jihar Bauchi inda suka tafka barna
  • Mazauna yankin sun sanar da yadda suka dinga harbi tare da saka tsoro a zukatan jama’a kafin su aiwatar da mugun nufinsu
  • Sun halaka wani shugaban yanki tare da wasu mutum hudu yayin da suka yi garkuwa da wani Daniel a yankin

Bauchi - ‘Yan bindiga sun kutsa yankin Gambar Sabon Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa da ke Bauchi inda suka halaka a kalla mutane biyar.

Taswirar Bauchi
Bauchi: ‘Yan Bindiga Sun Halaka Rayuka 5, Sun Sace Mutum 1. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Sun yi garkuwa da mutum daya a farmakin da suka kai inda suka bar mazauna wurin cikin rudani.

Jaridar Punch ta gano daga mazauna yankin da suka bukaci a boye sunansu cewa, ‘yan bindiga sun dira yankin a daren Asabar tare da harbi babu kakkautawa a iska wanda hakan ya tsorata jama’a kafin su aikata mugun abun.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Yace miyagun sun yi garuwa da wani Daniel tare da halaka shugaban yankin da wasu mutum hudu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazaunin yankin mai suna Manasseh Danladi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yace:

“Eh lamarin ya faru da gaske. A ranar Asabar, wasu mutane sun zo kauyenmu inda suka halaka kawuna da wasu mutum hudu yayin da suka tasa keyar Daniel.”

Karin bayani na tafe…

Asali: Legit.ng

Online view pixel