Tinubu Ya Watsawa Majalisa Ƙasa a Ido, Ya Ƙi Sanya Hannu kan Sababbin Ƙudurori 2

Tinubu Ya Watsawa Majalisa Ƙasa a Ido, Ya Ƙi Sanya Hannu kan Sababbin Ƙudurori 2

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa da kudurori biyu da Majalisar Tarayya ta amince da su saboda kura-kurai da suka saɓa wa kundin mulki
  • Tinubu ya ce kudurin bincike kan albarkatun ƙasa ya ƙunshi matsalolin tsari da rubutu da ya kamata a gyara kafin a ce ya sanya hannu a kansa
  • Shugaban ya ce bayan an yi gyaran da ya dace, zai iya sanya hannu domin kudurorin su zama doka, amma a yanzu ba zai iya rattaba hannun ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙi rattaba hannu kan kudurori biyu da Majalisar Tarayya ta amince da su, yana mai cewa suna ɗauke da wasu kura-kurai da kuma batutuwan da suka saɓa wa kundin tsarin mulki, waɗanda dole sai an gyara su kafin su zama doka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi watsi da kudirori 2 da majalisa ta aiko, ya ki sa hannu su zama dokoki

An sanar da Majalisar Dattawa matakin shugaban ƙasar ne ta wasiƙu guda biyu da shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Shugaba Tinubu ya ki amincewa da wasu kudurori 2
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a majalisar hadin gwiwa ta tarayya, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya ki amincewa da kudurori 2

Kudurorin da abin ya shafa sun haɗa da Raw Materials Research and Development Council (Amendment) Bill, 2026 da kuma Chartered Institute of Purchasing and Supply Management of Nigeria Bill.

A cikin wasiƙarsa, Tinubu ya ce ya ƙi amincewa da kudurin ne bisa tanadin Sashe na 58(4) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya ba shugaban ƙasa ikon mayar da kuduri ga Majalisar Tarayya idan ya ga akwai matsaloli.

Shugaban ya ce taken kudurin bai bayyana ainihin manufarsa ba, wato bunƙasawa, karewa da kuma sarrafa albarkatun ƙasa na Najeriya tare da ƙarfafa masana'antun cikin gida.

Ya kuma ce akwai rashin daidaito a Sashe na 2 na kudurin, inda aka haɗa manufofin doka da ayyukan da ya kamata hukumar ta riƙa gudanarwa, abin da ya sa tsarin kudurin ya rikice.

Tinubu ya ƙara da cewa wasu sassan da suka shafi ƙara wa albarkatun ƙasa ƙima an saka su a wuraren da suka shafi kuɗaɗen hukumar da asusun shekara-shekara, abin da ya sa kudurin ya rasa daidaito.

Kara karanta wannan

Matasa sun tura saƙo ga Tinubu da 'yan bindiga suka ƙona garuruwa 7 a jihar Neja

Tinubu ya soki wasu tanade-tanaden CIPSMN

Shugaban ƙasar ya kuma ƙi amincewa da kudurin Chartered Institute of Purchasing and Supply Management of Nigeria, yana mai cewa wasu tanade-tanadensa sun bai wa cibiyar ikon da ya wuce abin da doka ta tanada.

Duk da yabawa da wasu gyare-gyaren da aka gabatar, Tinubu ya ce akwai buƙatar sake nazarin wasu sassa kafin ya sanya hannu.

Ya yi ƙorafi musamman kan wani tanadi da zai tilasta wa kamfanoni da ƙungiyoyi sanar da cibiyar cikin wata guda idan sun naɗa shugaban sashen saye da sarrafa kayayyaki.

Shugaba Bola Tinubu ya ce idan majalisa ta gyara kudurorin to zai iya amincewa da su
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a majalisar hadin gwiwa ta tarayya, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya ba majalisa shawara

A cewarsa, cibiyar ba ita ce ke kula da waɗannan kamfanoni ba, don haka ba za ta iya tilasta musu su bayar da irin waɗannan bayanai ba.

Haka kuma, shugaban ya ce bai dace a ba cibiyar ikon binciken kamfanoni, ladabtar da ma'aikata ko tabbatar da bin ƙa'idoji a kan kamfanonin da aka kafa ƙarƙashin Companies and Allied Matters Act (CAMA) ba, domin hakan ya zarce ikon da doka ta ba ta.

Kara karanta wannan

An yi wa Amurka kaca kaca a kofin duniya duk da shiga da fitar Trump a boye

Duk da ƙin amincewar da ya nuna, Tinubu ya bayyana cewa zai iya rattaba hannu kan kudurorin idan Majalisar Tarayya ta gyara matsalolin da ya nuna.

Tinubu ya mika fom ga APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen duk wata jita-jita da jama'a ke yaɗa wa kan wanda zai dauka a matsayin abokin takara a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa APC ta karbi takardun tsayawa takarar Tinubu da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma da Abba Kabir Yusufa na Kano na cikin gwamnonin d suka halarci taron da APC ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com