Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yanka shugaban Karamar Hukuma Bayan Karban Kudi

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yanka shugaban Karamar Hukuma Bayan Karban Kudi

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko waye ba sun fille kan Chris Ohizu, shugaban karamar hukumar Ideato ta arewa a jihar Imo
  • Makasan Ohizu sun halaka shi ne bayan sun karbi kudin fansarsa naira miliyan 6 kuma sun sha alwashin ba za a yi zabe ba
  • An gano batun kisan nasa ne bayan maharan sun daura bidiyon a Whatsapp din marigayin

Yan bindiga sun guntule kan Chris Ohizu, shugaban karamar hukumar Ideato ta arewa a jihar Imo, bayan sun yi garkuwa da shi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an kashe shugaban karamar hukumar ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu, bayan wadanda suka yi garkuwa da shi sun karbi kudin fansa naira miliyan 6.

Jihar Imo
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Yanka shugaban Karamar Hukuma Bayan Karban Kudi Hoto: Punch
Asali: UGC

A cikin wani bidiyo da ya yadu, makasan dan siyasar sun ce lallai ba za a yi zabe ba kasar nan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Yadda aka kashe shi, majiya

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta a karamar hukumar, ta bayyana cewa makasan nashi sun wallafa bidiyon faruwar lamarin a kan wayar mamacin ta hanyar daurawa a manhajar Whatsapp dinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"An fille kan shugaban karamar hukumar. Mun ga bidiyon yadda aka fille masa kai a ranar Lahadi. Makasansa sun daura shi a kan Whatsapp dinsa. Ta yadda mutane suka san batun guntule masa kan kenan.
"Bidiyoyin sun yi muni. An daure shi kusan rabi tsirar kafin suka yanke masa kai. Wannan shine mafi radadin mutuwa. Sun kwankwatsa shi bayan sun karbi miliyan N6 kudin fansa."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da lamarin kuma a takaice ya ce "ana gudanar da bincike."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Yi Babbar Ɓarna a Jiha

An yi garkuwa da marigayin a ranar Juma'a tare da wasu mutum biyu bayan an kona gidansa da ke mahaifarsa a garin Imoko yankin Arondizuogu.

An harbe shi kafin aka yi awon gaba da shi rahoton The Eagle.

Yan sanda sun kama matasa 33 kan kisan basarake da kona ofishin yan sanda a Neja

A wani labarin kuma, mun ji cewa jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun yi nasarar cafke wasu matasa da ake zargi da kisa dagacin Lambata a karamar hukumar Gurara ta jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel