Na Allah Ba Su Karewa: Dan Sanda A Kano Ya Ki Karbar Cin Hanci Na Naira Miliyan 1 Don Sakin Mai Garkuwa

Na Allah Ba Su Karewa: Dan Sanda A Kano Ya Ki Karbar Cin Hanci Na Naira Miliyan 1 Don Sakin Mai Garkuwa

  • Wani Alhaji Bamuwa Umaru dan shekaru 62 ya shiga hannun yan sandan jihar Kano kan yunkurin ba wa dan sanda cin hanci
  • Umaru ya yi kokarin bawa SP Aliyu Mohammed na tawagar yaki da masu garkuwa N1m ne ya saki wani Yusuf Ibrahim da aka kama kan zargin garkuwa da mutane
  • Yusuf Ibrahim, wanda aka kama a tasha bayan wani direba ya gane shi a matsayin wanda ya sace shi ya amsa cewa shi mai garkuwa ne

Jihar Kano - Yan sanda sun kama wani mutum dan shekaru 62, Bamuwa Umaru kan yunkurin karbo wani da ake zargi da garkuwa da mutane, Yusuf Ibrahim, Vanguard ta rahoto.

Kakakin yan sanda, SP Abdullahi Haruna, a ranar Talata ya ce an kama Umaru bayan ya yi dan sanda tayin cin hanci na Naira miliyan 1 don a saki wanda ake zargin, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Fadawa 4 na fitaccen sarki a Arewa sun kone kurmus a hadarin mota

Taswirar Jihar Kano
Dan Sanda A Kano Ya Ki Karbar Cin Hancin N1m Daga Mai Garkuwa Da Mutane. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haruna ya ce binciken farko da aka fara ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yana da hannu wurin garkuwa da mutane a kauyukan Katsina da Zamfara kuma ya amsa cewa tawagarsa sun kashe har mutum 10 cikin wadanda suka sace, shi da kansa ya halaka biyu.

Kakakin yan sandan ya ce:

"A ranar 16 ga watan Disamba misalin karfe 2 na rana, wani Alhaji Bamuwa Umaru, dan shekara 62, mazaunin Shika, karamar hukumar Sabon gari, Jihar Kaduna ya tuntubi SP Aliyu Mohammed na tawagar yaki da masu garkuwa ya bashi N1m a matsayin cin hanci don sakin wani Yusuf Ibrahim, dan shekara 27, mazaunin kauyen Danjibga, karamar hukumar Tsafe, Jihar Zamfara, da aka kama kan garkuwa a tashar Rijiyar Zaki, Kano.
"Tawagar Operation Restore Peace karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, DPO na rundunar yan sandan Rijiyar Zaki na Kano bayan wani direba da suka taba sacewa kan hanyar Funtua-Gusau ya gane shi, ya ce sai da suka biya N500,000 kafin aka sako shi.

Kara karanta wannan

Kano: Rayuka 2 na Matasan da Suka je Gyara Sokaway a Kano Sun Salwanta Bayan Sun Kasa Fitowa

Mun kashe a kalla mutum 10, na kashe uku cikinsu, wanda ake zargi

"Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya yi garkuwa da mutane a kauyukan Sheme, Yankara, Faskari da Kucheri a Jihohin Katsina da Zamfara. Ya cigaba da kashe shi da tawagarsa sun kashe a kalla mutum 10, kuma shi kansa ya kashe biyu cikinsu."

Ya kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin bayan kammala bincike.

Haruna ya ce kwamishinan yan sanda, CP Mamman Dauda, ya gode wa mutanen Kano da sauran jami'an tsaro, kafaffen watsa labarai, yan bijilante da masu ruwa da tsaki bisa addu'a da goyon baya da tallafi da hadin kai.

An kama masu garkuwa yayin kokarin karbar kudin fansa a Gombe

Yan sandan Jihar Gombe sun gabatar da wani Mohammed Aminu da Salisu Sa'idu, wadanda aka kama yayin karban kudin fansa N300,000 daga yan uwan wanda suka sace

Kara karanta wannan

Haren-haren da ake kaiwa cikin daji mata da yaran Fulani kawai ake kashewa, Gumi

Mahid Abubakar, kakakin yan sanda ya ce an cafke masu sace mutanen ne bayan sun karbi N100,000 daga yan uwan wani Jibril Mohammed.

Asali: Legit.ng

Online view pixel