Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya

Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya

  • Wasu yan bindiga sun kutsa fadar Agwom Izere, Dr Isaac Wakili sun sace shi a Plateau
  • Wani mazaunin unguwar da abin ya faru ya ce maharan sun kashe dan bijilante daya sun kuma harbi dan sanda
  • Rundunar yan sandan jihar Plateau ta tabbatar da sace sarkin ta kuma ce jami'anta na kokarin ceto shi

Jihar Plateau - Yan bindiga sun sace sarki mai daraja ta daya a jihar Plateau, Dr Isaac Azi Wakil, Agwom Izere, rahoton Leadership.

Wakili shine babban sarkin mutanen Izere da ke karamar hukumar Izere a karamar hukumar Jos East a jihar.

Plateau
Yan Bindiga Sun Tafi Har Fada Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Daya A Arewa, Sun Kashe Mutum Daya. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

The Punch ta rahoto cewa an sace sarkin mai daraja ta farko ne a safiyar ranar Juma'a a lokacin da yan bindiga suka kutsa fadarsa da ke Shere.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Tagwayen Abubuwa Masu Fashewa Sun Tashi a Wurin Kamfen din APC a Fatakwal, 3 Sun Jigata

Wani mazaunin garin, Philip Izam, ya tabbatarwa The Punch sace sarkin a Jos a ranar Juma'a.

Izam ya ce a lokacin da aka kawo harin, an kashe mutum daya kuma an raunata wasu sakamakon musayar wuta da aka yi da maharan da jami'an tsaro da suka yi kokarin ceto sarkin.

Izam ya ce:

"Zan iya tabbatar mama cewa an sace Mai martaba Isaac Wakili, Agwom Izere. Yana fadarsa da ke Shere lokacin da masu garkuwan suka kutsa fadarsa misalin karfe 1.30 na dare.
"Yan bindigan sun yi musayar wuta da masu tsaron fadar suka ci galaba kansu. An tura karin yan sanda da wasu jami'an tsaro, an yi musayar wuta amma yan bindigan sun tafi da sarkin.
"Daya cikin yan bijilante da yan bindigan suka harba ya rasu, an har wani dan sanda amma yana da rai."

Yan sandan Plateau sun tabbatar da sace Sarkin

Rundunar yan sandan Plateau ta bakin kakakinta, Alabo Alfred, ita ma ta tabbatar da sace sarkin.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Jiga-Jigan Jam'iyar APC Mai Mulki

A cewarsa, za a tura karin jami'an tsaro zuwa garin kuma muna aiki don ganin an ceto sarkin da aka sace.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa:

"A halin yanzu da na ke magana, jami'an mu suna bincika dazuka don tabbatar an ceto sarkin tare da hukunta wadanda suka sace shi.
"Muna kuma kira ga al'umma su rika taimaka mana da bayanai masu amfani don taimaka mana dakile irin hakan kafin ya faru."

Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Sarki A Kaduna

Kun ji cewa wasu yan bindiga sun kai hari gidan marigayi Sarkin Jere, Dakta Sa'ad Usman da ke karamar hukumar Kagarko.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun sace wani mutum mai suna Hussaini da matsarsa har da dansu dan wata hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel