Masu Garkuwa Da Mutane
Wani dan bindiga ya gamu da tsautsayi yayin da ya je sace makwabcinsa, Alhaji Mohammed Makasudi a jihar Neja, mai gidan ya harbe shi a kafa yayin sace shi.
Tsohuwar minista a lokacin gwamnatin Buhari, Sadiya Farouk ta shiga jerin masu gangami don ceto daliban da aka sace a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke jihar Zamfara.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi kakkausan martani kan sace kwamishinan watsa labarai na jihar da wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ukum ta jihar.
'Yan bindiga sun sace daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Zamfara, a wannan rahoto mun tattaro muku dukkan daliban da aka ceto zuwa yanzu daga maharan.
Masu garkuwa sun sace Kwamishinan yada labarai da al'adu a jihar Benue, Matthew Abo a daren jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Zaki-Biam.
Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta samu nasarar cafke miyagun ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa waɗanda ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane.
Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a Jami'ar Gwamnatin Tarayya a Gusau tare da sace dalibai a dakunansu na kwana har guda uku a daren jiya da misalin 3 na dare.
Masu garkuwa da mutane sun hari kauyen Dogon Noma da ke Maro, a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum biyu tare da garkuwa da wasu uku.
Jami'an tsaro sun samu nasarar ceto mutane masu yawa da miyagun ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari