Rundunar Tsaro A Najeriya Ta Nemi Hadin Kan Jama'a Don Dakile Matsalar Tsaro

Rundunar Tsaro A Najeriya Ta Nemi Hadin Kan Jama'a Don Dakile Matsalar Tsaro

  • Rundunar tsaron Najeriya ta nemi hadin kan al'umma wurin yakar ta'addanci da kuma 'yan bindiga da ke cin karensu ba babbaka
  • Rundunar ta bayyana haka ne a yau Alhamis 28 ga watan Satumba a Abuja inda ta ce sojoji kadai ba za su iya dakile matsalar ba
  • T bukaci hadin kan mutane daidaku inda su ka ce rashin hadin kan na daga cikin babbar matsalar da su ke fuskanta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hedkwatar rundunar tsaro a Najeriya ta bayyana cewa ba za ta iya dakile matsalar tsaro ba ita kadai.

Ta ce matsalar ta'addanci da garkuwa da mutane ba aikin jami'an tsaro ba ne kadai ya na bukatar hadin kan jama'a.

Sojoji kadai ba za su iya dakile matsalar tsaro ba, Rundunar tsaro
Ta'addanci: Rundunar Tsaro A Najeriya Ta Nemi Hadin Kan Jama'a. Hoto: Hedkwatar Tsaro.
Asali: UGC

Meye rundunar tsaron ke cewa kan ta'addanci?

Daraktan yada labarai na hukumar, Manjo Janar Edward Buba shi ya bayyana haka a yau Alhamis 28 ga watan Satumba a Abuja.

Kara karanta wannan

Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ya Shiga Tangal-Tangal, Rigima Ta Kai Gaban Alkali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce masu aikata ta'addanci da tada zaune tsaye a cikin al'umma su ke don haka da hadin kan jama'a ne kadai za a iya yin nasara, The Nation ta tattaro.

Sanarwar ta ce:

"Kawar da matsalar ta'addanci da masu garkuwa da mutane ba aikin sojoji ne kadai ba.
"Ya tabbata cewa rundunar sojoji kadai ba za ta iya kawo karshen matsalar ta'addanci ba a kasar.
"Masu aikata wannan laifuka a cikin al'umma su ke kuma su na da 'yan uwa da abokan arziki a inda su ke zama."

Wane sako rundunar tsaron ta tura kan ta'addanci?

Hukumar ta ce wannan rashin ba da goyon baya na al'umma shi ya ke kawo cikas wurin dakile matsalar tsaro a Najeriya, Newsdiary ta tattaro.

Sanarwar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Wike ya kori manyan jami'an hukumomi da kamfanonin FCTA

"Ta hanyar hadin kai ne kawai za mu hana masu aikata laifuka sakat a kasar ba ki daya."

Rundunar ta ce ko kadan sojin kasar ba su damu ba barazanar 'yan bindigan ba saboda sun riga sun gano lagonsu kuma ba su da wani karfi sai na kisa.

'Ku mika wuya ko mu hallaka ku', Sojoji ga 'yan bindiga

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta tura gargadi ga 'yan bindiga da masu tada zaune tsaye.

Rundunar ta ce dole 'yan ta'addan su mika wuya ga rundunar ko kuma su hallaka su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel