Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Kwamishinan Yada Labarai A Jihar Benue

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Kwamishinan Yada Labarai A Jihar Benue

  • Jimamai yayin da 'yan bindiga su ka sace kwamishinan yada labarai da al'adu a jihar Benue
  • An sace Matthew Abo ne a daren jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Zaki-Biam
  • Tahav Agerzua, mai ba da shawara ga tsohon gwamnan jihar, shi ya bayyana haka a shafinsa na Twitter

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Benue - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yada labarai da al'adu, Matthew Abo a jihar Benue.

Maharan sun sace Abo ne a gidansa da ke Zaki-Biam a karamar hukumar Ukum da ke jihar.

'Yan bindiga sun sace kwamishina a jihar Benue
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Kwamishina A Benue. Hoto: The Guardian.
Asali: Facebook

Yaushe aka sace kwamishinan a Benue?

An sace Abo ne daren jiya Lahadi 24 ga watan Satumba yayin da masu garkuwan su ka zo a babura guda hudu, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda aka sacen an rantsar da shi a matsayin sabon kwamishina a jihar a ranar 29 ga watan Agusta.

Karamar hukumar Ukum da ke jihar inda kwamishinan ya fito ta kasance mafakar 'yan bindiga da dama inda ake aika-aika da sace-sace.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamishinan ya shiga hannun 'yan bindigan sun kai farmakin ne a kan babura guda hudu tare da sace kwamishinan a cikin gidansa.

Meye martani 'yan sanda kan sace kwamishinan a Benue?

Tahav Agerzua, Hadimin tsohon gwamnan jihar ya bayyana cewa 'yan bindigan sun kai farmaki gidan kwamishinan tare da umartan kowa ya kwanta kasa inda su ka tafi da shi.

Ya kara da cewa maharan sun tilasta kwamishinan hawa bayan daya daga cikin masu baburan inda su ka tsere da shi, cewar Vanguard.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ba ta ce komai ba game da harin bayan tuntubarta da aka yi.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Malaman jami'a sun ci taliyar karshe saboda aikata badala da rashawa

Har ila yau, Sakataren yada labarai na Gwamna Alia Hyacinth, Kula Tersoo ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

'Yan bindiga sun sace fasinjoji 10 a motocin gwamnatin jihar Benue

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace fasinjoji akalla 10 da ke cikin motocin gwamnatin jihar Benue da su ke kan hanyarsu ta zuwa Legas.

Maharan sun kai farmaki kan matafiyan ne a hanyar Okene da ke jihar Kogi bayan sun baro Makurdi babban birnin jihar Benue.

Jihar Benue na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara da ke kewaye da jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel