Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane Mutum 20 a Jihar Taraba

Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane Mutum 20 a Jihar Taraba

  • Jami'an ƴan sanda a jihar Taraba sun samu nasarar cafke masu garkuwa da mutane har mutum 20 a jihar
  • Kakakin rundunar ƴan sanda na jihar ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun karɓi kuɗin fansa kusan N30m
  • Kakakin ya bayyana cewa waɗanda ake zargin duk sun amsa laifukansu inda za a gurfanar da su a gaban kuliya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Taraba - Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta cafke aƙalla mutum 20 da ake zarginsu da aikata laifin yin garkuwa da mutane a jihar, cewar rahoton Channels tv.

Ƴan ta'addan sun shiga hannun jami'an tsaron ne bayan sun samu bayanan sirri da ƙorafe-ƙorafe da jama’a suka yi kan munanan ayyukan masu garkuwa da mutanen, wanda hakan ya sanya rundunar ta shiga farautar miyagun a maɓoyarsu.

Kara karanta wannan

Yan Majalisa Sun Karbi Cin Hanci Domin Tsige Mataimakin Gwamnan APC? Gaskiya Ta Bayyana

Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane a jihar Taraba
Babban sufetan yan sanda na kasa, Kayode Adegbotokun Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar ƴan sandan da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin duk sun amsa laifin da ake tuhumarsu da su.

An ƙwato makamai masu yawa a hannunsu

Kakakin ya kuma bayyana cewa jami'an rundunar sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da kuma wata bindiga mai jigida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, waɗanda ake zargin sun karɓi sama da naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa daga iyalan mutanen da suka riƙa yin garkuwa da su, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ƴan sanda za su cigaba da farautar ƴan ta'adda

Kakakin ya bayyana cewa rundunar ƴan sandan ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen fatattakar ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a jihar.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

A kalamansa:

"Rundunar ƴan sanda ba ta ja da baya ba a kokarinta na ci gaba da farautar ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar bisa umarnin babban sufeton ƴan sanda Kayode Egbetokun."
"Ina so in tabbatar muku cewa rundunar a ƙarƙashin kulawar CP Yusuf Suleiman ta himmatu wajen bin duk hanyoyin da suka dace domin magance aikata miyagun laifuka da inganta tsaro a jiha."

Kakakin ya kuma bayar da tabbacin cewa za a gurfanar da dukkanin waɗanda ake zargin a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka.

Jami'an tsaro na ƙoƙari

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba, wanda ya yaba da ƙokarin da jami'an tsaro ke yi wajen ganin sun murƙushe ƴan ta'adda a jihar.

Malam Hassan Kundi ya bayyana cewa a cikin ƴan kwanakin nan an ɗan samu matsalar tsaro a jihar amma jami'an tsaro sun matsa ƙaimi wajen magance matsalar.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: Dakarun Sojoji Sun Gano Masana'antar Ƙera Bindigu a Jihar Arewa, Sun Kama Mutum 2

"Eh tabbas an ɗan samu matsalar tsaro a cikin ƴan kwanakin nan, amma an samu cigaba sosai wajen magance matsalar saboda ƙoƙarin da jami'an tsaro suke yi." A cewarsa.

Yan Bindiga Sun Sace Likita a Kogi

A wani labarin kuma, wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani likita a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun cafke Austin Uwumagbe, darektan asibitin Victory Hospital da ke Ogaminana, a ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi bayan ya tashi daga wajen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel