Masu Garkuwa Da Mutane
Matasa a Najeriya sun yabi Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle da babban Minista Badaru Abubakar kan inganta tsaro a kasar Najeriya baki daya.
Masu garkuwa sun sace wani Farfesa a Jami'ar Calabar da ke jihar Kuros Riba mai suna Patrick Egaga a daren jiya Lahadi 12 ga watan Nuwamba a gidansa.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin da ƴan ta'adda suka kai a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar. Sun ceto mutum uku da aka sace.
Wani ma’aikacin hukumar INEC da aka yi ram da shi a ranar jaji-birin zaben Gwamnonin jihohi, ya samu ‘yanci. Sanarwa ta fito daga INEC cewa malamin zaben ya tsira.
Jami'an tsaro na ƴan sakai sun samu nasarar halaka masu garkuwa da mutane mutum huɗu a wani artabu da suka yi a jihar Kebbi bayan sun kai musu sumame.
Idan manomi ya yi sa'a gonarsa ta yi kyau, sai ya biya kusan N100, 000 kafin ya yi girbi. ‘Yan bindiga na karba a hannun manoma kafin a cire kayan gona a Kaduna.
Kwanaki kadan bayan sace mutanen a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, wasu daga cikin jariran guda biyar sun mutu yayin da su ke hannun 'yan bindiga.
Dillalan kasuwar shanu a jihar Abia sun zargi gwamnatin jihar da mu su sharri don samun damar korarsu a jihar gaba daya, sun karyata samun gawarwarki a kasuwar.
Wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wani mai sarautar gargajiya tare da sace matarsa da dansa da kuma wasu mutane takwas a kauyukan da ke makwabtaka da su.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari