Benue: Masu Garkuwa da Kwamishina Sun Nemi Kudin Fansa N60m

Benue: Masu Garkuwa da Kwamishina Sun Nemi Kudin Fansa N60m

  • Masu garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Benuwai sun turo saƙo mai ɗaga hankali ta wayar ɗaya daga cikin iyalansa
  • Yan bindigan sun nemi a lalubo musu kuɗi Naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa kafin su sako Mista Mathew Abo
  • Tun ranar Lahadi da ta gabata aka sace kwamishinan daga gidansa, kuma har kawo yanzu yana hannun masu garkuwa da mutane

Jihar Benue - 'Yan bindigan da suka yi garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai, al'adu da wuraren buɗe ido na jihar Benuwai, Mathew Abo, sun aiko da saƙon abin da suke buƙata.

Daily Trust ta ce waɗanda suka yi garkuwa da Kwamishinan sun fara tattauna wa da iyalansa ranar Asabar, inda suka nemi a haɗa Naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa.

Yan bindiga sun nemi fansar kwamishinan da suka sace.
Benue: Masu Garkuwa da Kwamishina Sun Nemi Kudin Fansa N60m Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun faɗi buƙatarsu ne ta hanyar kiran wayar ɗaya daga cikin mambobin iyalan kwamishinan.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Fallasa Matsalar da Ta Hango Gabanin Zaben Gwamna a Jihohi 2

Hadimin midiya na tsoffin gwamnonin jihar Benuwai biyu, Mista Tahav Agerzua, ya cw wanda 'yan bindigan suka kira wayarsa ya nemi a ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun koma gallazawa kwamishinan domin su tilasta a biya musu bukatarsu, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Ya kuma ce majiyar iyalan ta ce masu garkuwan sun kira waya inda suka sanya kiran a kan lasifika domin dangi su ji kukan kwamishinan yana neman agaji.

Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da kwamishinan ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan sun farmaki gidansa a kan babura hudu.

Rahoto ya nuna lokacin da suka shiga gidan, sun umarci kowa da kowa a gidan ciki har da matar kwamishinan da ‘ya’yansa da su kwanta, suka tafi da shi inda ba a sani ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Ƙazamin Hari Jihar Kaduna, Sun Halaka Mutane da Yawa

Wane mataki gwamnati da jami'an tsaro suka dauka?

Tun da farko, Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya yi Allah wadai da sace kwamishinan, kuma ya umarci jami'an tsaro su bi diddigin 'yan bindigan.

Yayin da aka tuntuɓi kakakin hukumar 'yan sanda reshen jihar, SP Catherine Anene, ba ta ɗaga kira ko amsa saƙonnin da aka tura mata kan lamarin ba.

Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Nauyin Yaron da Yan Bindiga Suka Kashe Mahaifinsa

A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki nauyin ƙaramin yaron nan da ya yi barazanar ɗaukar fansar kisan mahaifinsa kan yan bindiga.

Ma’aikatar Mata, Ƙananan yara da Ci gaban Jama’a ta jihar Zamfara ta yi alkawarin daukar nauyin karatun yaron da kuma walwalarsa ta yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262