Kwamishina A Jihar Benue Ya Shaki Iskar 'Yanci Bayan Shake Kwanaki A Hannun 'Yan Bindiga

Kwamishina A Jihar Benue Ya Shaki Iskar 'Yanci Bayan Shake Kwanaki A Hannun 'Yan Bindiga

  • Kwamishinan yada labarai a jihar Benue ya kubuce daga hannun 'yan bindiga da safiyar yau Alhamis
  • An sace Matthew Abo ne a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Zaki-Biam a jihar Benue
  • Kwamishinan ya dawo gida da misalin karfe daya na dare duk ba a bayyana ko an biya kudin fansa ba ga maharan

Jihar Benue - Kwamishinan yada labarai da al'adu a jihar Benue, Matthew Abo ya shaki iskar yanci.

An saki kwamishinan ne da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Oktoba bayan shafe kwanaki a hannun mahara.

Kwamishina a jihar Benue ya shaki iskar 'yanci a yau
Kwamishinan Jihar Benue Ya Shaki Iskar 'Yanci. Hoto: Tahav Agerzua, NPF.
Asali: Facebook

Yaushe aka sace kwamishinan a jihar Benue?

An sace Abo a daren ranar Lahadi 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Zaki-Biam.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615 da Attajiri Ya Tausayawa Mutanen Kano

Punch ta tattaro cewa kwamishinan ya dawo gida da misalin karfe 1 na dare a yau.

Wata majiya daga bangaren iyalinsa ba ta bayyana ko an biya wasu kudade ko sabanin haka ba, The Nation ta tattaro.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Catherine Anene ya ci tura yayin tattara wannan rahoto.

Ba a tabbatar ba ko Naira miliyan 60 da 'yan bindigan su ka nema an biya su kafin sakin kwamishinan ba.

Wane sako kwamishinan ya aike ga mutane?

Kwamishinan ya tabbatar da sakin nasa a yau Alhamis 5 ga watan Oktoba inda ya godewa Gwamna Alia Hyacinth na jihar da kuma jami'an tsaro.

Har ila yau, kwamishinan ya godewa 'yan uwa da abokan arziki da su ka taya da addu'a har zuwa lokacin fitowarshi, cewar Vanguard.

Ya ce:

"Ina godiya da irin taimako da addu'o'i da jama'a su ka taya ni da shi yayin da na ke tsare da kuma dawowa ta gida.

Kara karanta wannan

Shekaru 2 da Dauke Shi, Har Yanzu Babu Labarin ‘Dan Takaran Gwamna a Najeriya

"Wannan abin da ya dame ni ina fatan zai kara kaimi wurin dakile matsalar tsaro a ciki da wajen jihar Benue."

'Yan bindiga sun sace kwamishina a jihar Benue

A wani labarin, 'Yan bindiga masu dauke da makamai sun sace kwamishinan yada labarai da al'adu a jihar Benue.

An sace Matthew Abo ne a gidansa da ke Zaki-Biam a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel